HUJJOJIN TASHIN KIYAMA A KIMIYANCE
Hausawa na cewa “komai ya ke da farko yana da
karshe” haka nan cikin suratul Nasr Allah ya tunatar da mu cewa
Q103:1-2 “Ina rantsuwa da lokaci (time) lalle ne
mutum yana cikin hasara”
Wadannan maganganu na sama, idan muka yi musu duba
na nazari zamu gane cewa hakika duk wata halitta a doron kasa tana gaggawa ne
izuwa karshenta. Yadda a farkon lokaci babu kowa haka ma za’a wayi gari komai
ya kare wata rana.
Cikin ginshikan imani, Allah ya wajabta yarda da
ranar lahira kuma babu wani addini da bai jaddada haka ba, amma akasarin mutane
na jayayya da cewa idan an mutu za’a tashi. Allah cikin hikimarsa ya bamu
hujjoji na kimiyya a warwatse cikin Qur’ani wadanda suke tabbatar mana da cewa
lallai kiyama gaskiya ce. Bari mu duba wadannan hujjoji daki-daki. A farko dai
Allah ya fara da jan hankalin mu cikin suratul A’araf
Q7:185 “Shin ba su yi duba ba a cikin tsarin sammai
da kasa, da kuma dukkan abin da Allah ya halitta, kuma akwai alamun kasancewar
ajalinsu, hakika, ya matso? To da wane labari a bayansa suke yin Imani?
Wato Allah na kira da mu duba, a kimiyance, yadda
ya tsara halittar sama da kasa da kuma dukkan halittu da ya watsa cikinsu, shin
bamu ga alamu cewa al-kiyama ta kusa ba? Duk sanda Allah ya ce a duba abu, to
ba fa duban ido kawai yake nufi ba, a’a, kallo na ilimi. Idan muka duba sama,
cikin ginshikan abubuwa da ke tallafawa rayuwa a duniya akwai; Hasken rana,
rumfar dake mana kariya ta sama, maganadisu, iskar da muke shaka, juyawar
duniyoyi, bakaken taurari (Black holes) da sauran abubuwa wadanda bamu gano su
bama. Idan muka dauki rana, kimiyya ta tabbatar mana da cewa tana da gwargwadon
tsawon ranta (life span) kuma tabbas zata mutu. Ta yaya rana zata mutu? Allah
ya ce mana cikin Suratul Kiyama (lura da surar da Allah ya kawo zancen cikinta)
Q75:7-10 “To, idan gani ya dimauta (yayi kyalli),
kuma wata ya dusashe (sannan) aka tara (waje guda) rana da wata. Mutum zai ce a
ran nan “ina wurin gudu?”
Binciken kimiyya ya tabbatar da yadda taurari
irinsu Rana ke mutuwa; wato yayin da kwayoyin iskar da ke konewa a cikin rana
(hydrogen da helium) suka kone sai tayi bindiga ta tarwatse, yayin da ta watse
sai ta harba ragowar sinadaranta su yadu ta kowacce fuska. Wannan huci da ta
watso sai ya lakume dukkan duniyoyi da ke kusa da ita. Hasken wannan tarwatsewa
zai kashe idon duk wani mai kallo a lokacin saboda tsananin haskensa. A yanzu
baka iya kallo rana kai tsaye, me kake tsammani idan girmanta da haskenta ya
ninka sau dubbai yayin tarwatsewarta? (wannan shine kyalli da gani zai yi,
yadda ayar ta fada) A lokacin da hakan ya faru, kaga raa da wata an tara su
waje daya kenan kamar yadda ayar t ace. Allah ya ce mana cikin suratul Haqqa
Q69”13-14 “To, idan an yi busa a cikin kaho, busa
daya, Kuma aka dauki kasa (duniya) da duwatsu, kuma aka nika su nikawa daya”
Wato hucin rana, yayin da ta tarwatse, idan ya iso
duniya cikin kiftawa zai narkar da duniya da sauran duniyoyi na kusa, yadda
burbushinsu ma ba za’a iya gani ba. Rana da muke gani, wuta ce wadda bamu san
irinta ba ke ci a cikinta, harsunan wuta dake tasowa a sama-samanta daidai yake
da zafin bama-bamai irin na nukiliya guda Biliyan daya. A can cikin tsakiyarta
kuwa zafin dake ciki ya isa domin da zaka iya buncino kwatankwacin kan allura,
idan ka ajiye shi a Zaria, wallahi hucinsa kadai sai ya kone mutumin da ke
Kano. Don haka yayin da rana ta tarwatse, sunan duniyarmu kararriya.
Idan muka yo kasa-kasa kuma, wannan rumfa (Ozone
layer) da Allah ya samar don yi mana kariya, da hannayenmu gashi nan muna rusa
ta. Ta hanyoyin amfani da man fetur, da kona dazuzzuka, da sare bishiyoyi da
iskokin sarrafa na’urorin sanyi (CFC) a yanzu munyi wa wannan rumfa tamu ta
kariya illa, domin tun 1989 kashi 7% ya tafi kuma nan da 2050 zamu iya lalata
Karin kashi 6%. Rashin wannan sashe na wannan rumfa ya haifar da sabbin ciwukan
fata da bamu sansu ba a baya, shine kai haifar da wutar daji a sassa sannan ya
kawo dumamar yanayi yadda dumin duniya ke ta karuwa wanda sakamakonsa ke haifar
da ambaliyar ruwa da fari a sassa. Tekunan duniya na tumbatsa yadda nan da 2050
idan Karin kashi 6% ya tafi na wannan rumfa, kankara dake doron duniya kudu da
arewa zasu narke yadda tekuna zasu tumbatsa kuma garuruwan da ke gabar teku
irinsu Lagos zasu koma cikin teku.
A cikin suratul Dhukkan Allah ya yi mana wani
gargadi
Q44:10-11 “Saboda haka ka dakata, ranar da sama
zata zo da wani hayaki bayananne, yana rufe mutane, azaba ce mai radadi”
Wato sakamakon wannan dumamar yanayi, nan gaba
duniya zata fuskanci matsanancin sanyi yadda kankara zata mamaye kusan kashi 50
na nahiyoyin duniya. A wannan lokaci za’a fuskanci gagaruman hadarin kankara
(ice storms) wadanda zaka dinga ganinsu tamkar hayaki ya tokare
sararin samaniya. Wannan yanayi zai kassara na’urorin zamani yadda mutane zasu
koma kamar zamanin da kafin a sami ci gaban fasaha. Miliyoyi zasu hallaka,
wadanda suka tsira kuma zasu saduda su koma ga Allah. Tun farkon duniya Allah
ya tsara canzawar dumin duniya yadda wasu lokatai akan fuskanci dogon zamani na
tsananin sanyi (Ice age). Hujjojin kimiyya sun tabbatar da fara samuwar wannan
yanayi na tsananin sanyi tun kafin a halicci Dan Adam kimanin shekaru miliyan
570 da suka wuce. Dan Adam ya fara fuskantar wannan yanayi ne, kimanin shekaru
miliyan biyu da rabi da suka wuce, bayan ruwan dufana, yadda dumin duniya yayi
kasa sosai aka sami kankara ta mamaye duniya. Cikin hujjojin kimiyya na samuwar
wannan mamaye na kankara a doro duniya shine samun manyan tafkuna na ruwan dadi
a wurare cikin tsakiyar nahiyoyi kamar wannan tafki namu na Chadi. Iri-irinsu
na samuwa sakamakon bayan kankara ta janye, wuraren da ked a kwazazzabo kan
cika da ruwa sakamakon narkewar kankara. Don haka wannan aya tana tabbatar mana
da nan gaba za’a sake komawa wannan yanayi. Sai ayar ta ci gaba da cewa a aya
ta
Q44:15 “Lalle mu, masu janyewar azaba ne, a dan
lokaci kadan, lalle ku, masu komawa ne (ga laifin)”
Wato zuwa wani lokaci wannan yanayi na kankara da
tsananin sanyi zai kauce, duniya ta sake dumama mutane su samu kansu, amma
kash! Sai kuma a koma ga sabo. Amma dai ga gargadi na karshe a aya ta gaba
Q44:16 “Ranar da muke damka, damka mafi girma,
lalle mu masu azabar ramuwa ne”
A cikin wannan rukuni da duniyar mu ke ciki (solar
system) akwai gurabuzan duwatsu (Asteroid belt) da ke kewayen duniyar Jupiter,
wani lokaci idan duwatsun suka yi karo da juna sai wani ya balle daga kewayen
ya kama hanyarsa. A iri-irin wannan dutse ne kimanin shekaru 20,000 da suka
wuce wani ya fado a yankin hamadar Arizona wanda ya samar da wani wawakeken
rami. A kurkusan nan kuma, a 1937, wani dutsen ya kusa fadowa duniya Allah ya
kiyaye. Daya daga cikin hujjoji da suka nuna dalilin kaucewar kakannin
kadangare katsam daga duniya shine wani dutse irin wadannan wanda ya fado
duniya kimanin shekaru miliyan 65 da suka wuce. A yankin Yucatan na Mexico
wannan dutse ya fado kuma ramin da ya haifar ya kai fadin daga kano zuwa Kaduna
(200km). Ya haifar da turnukewar kura wadda ta kare hasken rana tsawon shekaru,
hakan ya saka mutuwar tsirrai saboda rashin hasken rana wanda das hi suke
sarrafa abinci. Rashin tsirrai kuma ya jawo halakar dabbobi na zamanin. Karfin
wannan fashewa daidai take da bam mai nauyin ton miliyan 30 (wato kamar
nukiliya 1500 wanda America ta jefawa japan a yakin duniya na
2). Bayan waccan kura day a haifar ya haifar da wutar daji mai girma
sakamakon wutar da ta kama bayan fadowar dutse, sannan kuma ya tukudo irin
mahaukaciyar guguwar nan ta teku wadda ake kira tsunami. Abin bai tsaya a nan
ba saboda wannan dutse yana dauke da wasu sanadirai masu guba wadanda ba a cika
samunsu a doron duniya ba. Dandazon wadannan matsaloli ne ya haifar da halakar
kimanin kasha 76 na duk nau’o’in halittun tsirrai da dabbobi na wancan zamani.
Iri-irin wadannan duwatsu na nan na shawagi a sararin sama jira suke Allah ya basu
umarnin inda zasu fada.
Akwai kuma bakake taurari (Black holes), wadanda
ba’a iya ganinsu saboda karfin maganadisun da ke cikinsu ko haske baya iya
kubcewa ya fito. Akwai irin wadannan taurari a tsakiyar kowacce dabaka, kuma
masana ilimin sararin samaniya sun gano su ne ta hanyar makwabtan wadannan
taurari. Duk da ba’a iya ganinsu kasancewar komai yazo kusa dasu suna zuke shi,
shi ya ba masana ikon gane cewa akwai su. Karfin maganadisun wadannan taurari
ya wuce tunani domin a kiyasce zaka iya gwada shi da nauyin kaya kimanin ton
miliyan goma (wato kamar motar tirela guda dari uku) idan ta fada cikin wannan
tauraro za’a dunkule su kamar kwalin ashana. Menene hikimar samar da su? Allah
ya ce mana cikin suratul Anbiya
Q21:104 “Ranar da muke nade sama kamar nadewar
takarda ga abubuwan rubutuwa, kamar yadda muka fara a farkon halitta haka zamu
mayar da ita. Wa’adi ne a kanmu. Lalle mu mun kasance masu aikatawa”
Ta yaya ake nade takarda ne? ana nade ta, ta hanyar
takure ta waje guda har sai ta dunkule waje guda, ko? To ta haka ne wadancan
bakaken taurari dake tsakiyar kowacce dabaka zasu zuke sauran taurari su
dunkule waje guda. Dabakar da tafi girma kuma ta hadiye karama har sai dukkan
sammai ta dunkule waje guda. A yayin da aka iso wannan gaba, shine ranar tashin
kiyama kuma Allah kadai ya san lokacin.
Comments
Post a Comment