Posts

SHIN AKWAI ALLAH?

Image
Mafi shahara cikin masana kimiyya a tarihin duniya, Albert Einstein, ya yi wasu maganganu guda biyu: Na farko “Kimiyyar da babu addini gurguwa ce sannan addini ba tare da kimiyya ba makaho ne” sannan ya ce “Kimiyya na iya bayanin yadda abubuwa su ke a zahiri amma ba za ta iya bayanin dalilin kasancewa yadda su ke ba” Addini da kimiyya sun kasance abubuwa guda biyu da su ka fi komai tasiri a rayuwar Dan Adam, duk da cewa kowanne akwai irin mahangarsa. Don haka ya kamata mu fahimci cewa abubuwa ne masu cikakkiyar alaka tamkar dai fuskoki guda biyu na kwabo. Alal misali mun san a kimiyance yadda sammai da kasa su ka samu kimanin shekaru biliyan 13 da su ka wuce daga tarwatsewar Big Bang, amma kimiyya ba ta da bayanin dalilin samuwar wannan sammai da kassai, addinai kadai ke iya wannan bayani. Mun san cewa a kimiyance duk hasken da ya daki madubi, kashi 95% ya kan dawo baya (reflect) amma kimiyya ba ta iya gane dalilin da ya sa ragowar kashi 5% ke ratsawa ta cikin madubin ya wuce. Don haka

RARRABEWAR NAHIYOYIN DUNIYA

Image
  Kimanin shekaru miliyan dari biyu das u ka wuce nahiyoyin duniya sun kasance a dunkule wuri guda kafin su fara rarrabewa, abinda ya samar da nahiyoyi shida da mu ke da su a yanzu. Rarrabewar nahiyoyi ya haifar da samuwar jerin carbin manyan duwatsu kusan a kowacce nahiya. An sami jerin carbin duwatsun Cordilleran a nahiyar Arewacin Amurka da kuma jerin duwatsun Andes a kudancin Amurka. Motsin Indiya wanda ya ci zango mai nisa ya haifar da jerin duwatsun Himalayas, jerin carbi mafi girma a duwatsun duniya inda ma ake da tsauni mafi tsawo (Mt. Everest). An sami jerin duwatsun  Alpine a Turai sakamakon jijjigar kudu da arewa tsakanin Afurka da Turai wanda kuma ya haifar da tekun Bahar Rum (Meditarranean sea). An sami jerin duwatsun Atlas a arewacin Afurka. Ta haka wadannan duwatsu su ka zama ginshikan da su ke rike da nahiyoyin kamar yadda Allah ya ce cikin suratul Naba’i: “Da duwatsu turaka (ga rike kasa)” Wasu da ga cikin hujjojin da su ka tabbatar da wannan al’amari a kimiyance s

RUWAN DUFANA

Image
Allah ya ba mu labarin mutanen farko cikin suratul Ma’ida: Q5:27 “Karanta musu labarin ‘ya’ya biyu na Adam da gaskiya, lokacin da su ka bada baiko, sai aka karba da ga dayansu kuma ba’a karba da ga dayan ba. Ya ce ”lallai ne zan kashe ka” dayan ya ce “Abin sani dai Allah na karba da ga masu takawa ne”  Allah ya fara ba mu labarin mutanen farko da nuna cewa su na da addini na bautar Allah wanda har baiko (Sacrifice) su na yi. Dalilin haka domin karyata masana tarihin asalin rayuwa da ke nuna cewa mutanen farko ba su san addini ba, wai sai a lokacin mutanen shu’aibu (Habilis) ne aka fara bauta. A aya ta gaba: Q5:30-31 “Sai ransa ya kawatar masa da kashe dan’uwansa sai kuma ya kashe shi, sannan ya wayi gari da ga masu hasara. Sai Allah ya aiki wani hankaka, ya na tono a cikin kasa domin ya nu na masa yadda zai binne gawar dan’uwansa. Ya ce “Kaitona na kasa in kasance kamar wannan hankaka domin in binne gawar dan’uwana” Binciken masana kimiyya ya nuna cewa mutanen farko (Afarensis)

GANGAR JIKIN DAN ADAM

Image
Allah ya ce mana cikin suratul Tin   95:4 “lalle mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa”  A halittun duniya babu wanda ya kai Dan Adam kyawon siffa sannan jikinsa yafi kowanne irin mashin da ka sani. Akwai yan rahoto (Receptors) miliyan hudu warwatse jikin fatarmu da ke banbance mana zafi, sanyi, tabawa ko ciwo. Fatarmu an yi ta rubi biyu don kare jiki daga bushewa da kuma adana ruwa da ke cikin jiki. Tana mana kariya daga sinadarai masu guba da kuma yanayi na sanyi ko zafi ta hanyar daidaita dumin jikinmu (temperature). A cikin bakin mu kan harshe, akwai kananan hudoji guda dubu tara wadanda ke taimaka mana banbance dandanon zaki, gishiri, tsami da sauransu. Jikin mutum na dauke da silin gashi miliyan biyar, wanda kowanne na iya Rayuwa ta akalla shekara 7. Wannan gashi, idan banda ta hanyar konewa, yana da wahala a iya lalata shi ta hanyar danshi ko ruwa ko amfani da wasu sinadarai. Kowanne sashe na jiki dandazon kwayoyin halitta (Cells) ne ya samar da shi, kuma cikin kowacce k

QUR’ANI DA KIMIYYA

Image
  Tsawon tarihin Dan Adam a doron kasa ya kasance mai fafutukar gano wanene shi, don me yake a nan duniya kuma shin menene makomarsa? Wadannan tambayoyi sun samo asali sakamakon nazarce-nazarce da shi Dan Adam yake yi a karan kansa da kuma dabbobin da suke kewaye da shi da kuma abubuwan halitta mara sa rai da ke sama da kasa. Wannan ya sa mutanen farko-farko suka kasance masu bautar abubuwan ban mamaki irinsu rana, taurari, hadari, tsawa dss wanda daga baya kuma sai aka rika sassaka gumaka domin su isar da bukatu ga ubangiji. Idan aka yi nazarin addinai masu bautar gumaka za a fahimci cewa suna amfani da gumakan ne a matsayin tsani zuwa ga ubangiji. Abubuwa mafi tasiri a cikin tarihin Dan Adam tun farkon lokaci zuwa yanzu abu biyu ne; Wato Addini da Kimiyya. Duk da kasancewar wadannan abubuwa sun kasance hannun riga da juna amma sun fi komai tasiri cikin rayuwar mutane. A yanzu ina ganin mun kai matsayin da zamu fahimci rayuwa mu kuma amsa wadancan tambayoyi da aka yi shekaru aru-a

WUTA

Image
Wuta, sinadari ce mafi mahimmanci a ginshikan samar da halittu da wanzuwarsu. Ba don wutar nan ba, da ni da kai da komai bai samu ba. Wuta  wata aba ce da ke samuwa sakamakon cudanyar kwayoyin zarra na iska da makamashi, haduwar wadannan kan haifar da zafi (heat) da kuma haske (light). A tarihin asalin halitta zamu ga cewa wuta ita ce ginshiki wajen canzawar kwayoyin zarra na farko mara sa rai. Kamar yadda muka gani cikin suratul fussilat Allah ya ce Q41:11 “Sannan ya daidaita zuwa ga sama alhali kuwa ita (a lokacin) hayaki ce” Allah ya fara kowacce halitta ne daga hayaki, wato wannan hayaki, binciken Kimiyya ya gano cewa shine hayaki mafi tsufa wato hayakin hydrogen (jinsin kwayoyin zarra na farko) domin ita ke da kashi 90% na yawan kwayoyin zarra a sammai da kassai. Wannan hayaki ya sami damar samar da halittun farko na taurari sakamakon dunkulewa waje guda a farkon lokacin halitta. Allah ya ce mana cikin Sutatul Anbiya Q21:30 “Shin wadanda suka kafirta ba su gani cewa lallai