RUWAN DUFANA
Allah ya ba mu labarin mutanen farko cikin suratul Ma’ida:
Q5:27 “Karanta musu labarin ‘ya’ya biyu na Adam da gaskiya,
lokacin da su ka bada baiko, sai aka karba da ga dayansu kuma ba’a karba da ga
dayan ba. Ya ce ”lallai ne zan kashe ka” dayan ya ce “Abin sani dai Allah na
karba da ga masu takawa ne”
Allah ya fara ba mu labarin mutanen farko da nuna cewa su na da
addini na bautar Allah wanda har baiko (Sacrifice) su na yi. Dalilin haka domin
karyata masana tarihin asalin rayuwa da ke nuna cewa mutanen farko ba su san
addini ba, wai sai a lokacin mutanen shu’aibu (Habilis) ne aka fara bauta. A
aya ta gaba:
Q5:30-31 “Sai ransa ya kawatar masa da kashe dan’uwansa sai kuma
ya kashe shi, sannan ya wayi gari da ga masu hasara. Sai Allah ya aiki wani
hankaka, ya na tono a cikin kasa domin ya nu na masa yadda zai binne gawar
dan’uwansa. Ya ce “Kaitona na kasa in kasance kamar wannan hankaka domin in
binne gawar dan’uwana”
Binciken masana kimiyya ya nuna cewa mutanen farko (Afarensis)
sakamakon kasusuwansu da aka tono a nan Afurka, sun rayu a duniya kimanin
shekaru miliyan uku da rabi kuma girmansu baya wuce mita daya da rabi. Girman
kwakwalwarsu kuwa bai wuce cubic centimetre 350 ba (Wato da kadan ta fi girman
kwakwalwar yaro). Qur’ani ya kara mana bayaninsu domin ya tabbatar mana su na
da yare kuma su na magana dashi. Sannan kuma su na da addini, sabanin fahimtar
masana kimiyya. Qur’ani ya tabbatar mana cewa karfin kwakwalwarsu ya na da
rauni, domin a lokacin ba su ma da ilimin binne gawa, kamar yadda sauran
dabbobo ke yi sai dai a yasar da ita har ta rube, sai da Allah ya turo hankaka
ya nuna masa. Allah dai shi ne mafi sani.
Mutanen da su ka zo bayan wadannan su ne mutanen Nuhu, kuma
Allah ya ba mu cikakken labarinsu. Mutanen Nuhu, masana kimiyya na kiransu da
Africanus saboda su ma a nan Afurka aka sami kasusuwansu. Babban abinda ya
banbanta su da mutanen farko shi ne yadda kwakwalwarsu ta habaka da ga cubic
centimetre 350 zuwa c.c. 400. Binciken kashinsu ya nuna cewa sun zauna a duniya
kimanin shekaru miliyan biyu da rabi, wato bayan karewar mutanen farko. Labarin
Annabi Nuhu da ruwan dufana, labari ne da babu wata al’umma da ba ta da irin
nata. Kusan dukkan addinai sun zo da labarin, amma babu inda aka bada labarin
da hujjoji na kimiyya kamar Qur’ani. Allah ya fara ba mu labarin cikin suratul
Ankabut:
Q29:14 “Lallai, mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa. Sai ya zauna a
cikinsu shekara dubu face hamsin”
Wata mu’ujiza ta Qur’ani shi ne kalma daya ko biyu na iya kunsar
wani fanni guda na ilimi. A wannan aya Allah ya ce Annabi Nuhu ya zauna tare da
mutanensa tsawon shekaru 950 kafin ma ayi ruwan dufana. Abu na farko shi ne mun
san cewa bayan ruwan dufana ma Nuhu yaci gaba da rayuwa kafin mutuwarsa don
haka hakikanin shekarunsa sun fi 950 kenan. Hikimar fada mana iya shekarun Nuhu
shi ne domin mu dada fahimtar cewa jinsin mutanensa ba fa irin mutanen da mu ka
sani bane, domin tsawon rai (Life span) ya na daga cikin gagaruman abubuwa da
su ke banbance jinsuna. Masana kimiyya na amfani da tsawon rai wajen rarrabe
azuzuwa na halittu. Misali mutum kamar ni ko kai bama iya rayuwa fiye da
shekara 100 zuwa 120, yayin da mutum ya wuce wadannan shekaru ya na zama tamkar
ba rayayye ba. Haka nan Biri baya wuce shekaru 40, Giwa ba ta wuce shekaru 80,
kare baya wuce 15. Kananan halittu irinsu kuda baya wuce kwana talatin, sauro
bai fi sati biyu ba, kwayoyin halitta da ke dakon jini a jikinmu ba sa wuce awa
12. Don haka tsawon rai wani gagarumin abu ne da ke banbance jinsuna (Species).
Babbar hikimar da Allah ya sa jinsu nan mutanen farko ke da irin wannan tsawon
rai shi ne, na farko dai kwakwalwarsu ba ta habaka sosai ba kuma mutane ba su
da yawa a lokacin, idan babu irin wannan tsawon rai sai jinsin Dan Adam ya kare
da wuri. Kuma jinsuna masu karanci dadewa sun fi saurin haihuwa. A cikin
suratul Hud Allah yaci gaba da labarin Nuhu:
Q11:37-38 “Ka sassaka jirgi bisa ganinmu da wahayinmu kuma kada
ka yi mini magana a cikin sha’anin wadanda su ka kafirta. Lallai su wadanda ake
nutsarwa ne. kuma ya na sassaka jirgin cikin natsuwa, a ko yaushe shugabanni da
ga mutanensa su ke wucewa ta gabansa sai su yi izgili
gareshi.”
Wannan ayoyi na ba mu hasken cewa a wannan lokaci ba’a san
sassaka ba don gashi manyan gari ma su na ganin kamar Nuhu ya hauka ce su na yi
masa dariya. Kuma Allah ya ce mana ita kanta sassakar jirgin karkashin wahayi
Nuhu ke yinta:
Q11:40 “Har a lokacin da umarnin mu ya je, kuma tanda ta bulbula.
Mu ka ce ka dauka cikinta da ga kowanne ma’aura guda biyu, da kuma iyalanka
face wanda magana ta gabata a kansa, da wanda ya yi imani”
Wannan bala’i na ruwa ba ya faru ya kare bane a wani dan
kankanin lokaci, abu ne da ya dauki lokaci mai tsawo. Allah ya umarci Nuhu ya
rika diban halittu na dabbobi da tsirrai (maza da mata) da kuma mutane. Saboda
ya kaddara ruwan zai halaka ilahirin halittu na wannan zamani ba ma mutane ba
kawai. Irin wadannan bala’o’i dasu Allah ke karar da wasu halittu don samar da wasu
kamar yadda na yi bayani a baya. Cikin suratul Qamar Allah ya ce:
Q54:11-12 “Sai mu ka bude kofofin sama da ruwa mai zuba. Kuma mu
ka bubbugar da kasa ta zama idanun ruwa. Sai ruwa ya hadu a kan wani
umarni da aka riga aka kaddara shi”
A sakamakon mamayewar da ruwa ya yi wa doron kasa, sai yanayin
duniya ya yi sanyi sosai, ababen da ke dumama duniya kamar zafin rana kuma
hadari ya rage shi sosai. Itatuwa kuma da ke fitar da iska su ka kasance
karkashin ruwa don haka sai ruwan ya fara daskarewa. Hujjojin tarihi na kimiyya
sun tabbatar da samuwar malalen kankara da ga cikin kogin Atalantika har zuwa
manyan duwatsun da ke karshen nahiyar arewacin Amurka. Kuma shi malalen wannan
kankara (Glaciation), babu gibi tsakaninsa. Akwai kuma malalen da ya tashi da ga
Arewacin duniya, wato da ga Greenland da Iceland ya yo gabas
har Kiev a kasar Russia daidai gabar kogin Dnieper. A
can gabashi kuma aka sami tuddan kankara na Siberia. Nahiyar Antaktika ita
ma sai ta daskare gaba daya (Wadda tafi girman nahiyar Turai), kuma tun da ga
wancan lokaci ta ke kankara har zuwa yau. A kudancin Amurka da ga
duwatsun Andes har zuwa New Guinea akwai kankara. A Afurka
wuraren gabashi, tsakiya da yammaci su ma duk sun sami malalen kankara
(Sakamakon wannan kankara ne ma aka sami tafkin nan na mu na Chadi). Sannan da
ga gabas ta tsakiya har zuwa manyan duwatsun himalayas sun kasance cikin
kankara. A takaice ko’ina cikin duniya ya sami wannan daskarewa. A cikin
suratul Hudu Allah ya ce:Q11:41 “Ku hau a cikin ta (jirgin Nuhu) da sunan
Allah ya yin da ta ke tafiya da ya yin da ta ke tsaye. Lallai ne Ubangijina,
hakika mai gafara ne mai jin kai”
Wannan aya na nuna mana cewa bayan wadanda aka saka cikin jirgin
Nuhu a lokacin da aka fara ruwa (Wato lokacin da jirgi ke tafiya), a ya yin da
ko’ina ma ya zama kankara an ci gaba da ceton halittu (shi ne ya yin da jirgin
ke tsaye). Allah ya kammala labarin da cewa:
Q11:44 “Ya kasa ki hadiye ruwanki, kuma ya sama ki kame. Kuma
aka fakar da ruwan, kuma aka hukunta al’amarin kuma jirgin ya daidaita
a kan judiyyi”
Ina ne Judi ta ke? Bincike ya nuna min cewa a cikin gundumar
Bohtan a kasar Turkiya ta yanzu akwai wani dutse da ake kira da Judi, kusa da
garin Jazirat Ibn Umar. Kuma a Kan iyakar Turkiya da Siriya akwai
wasu manyan duwatsu da ake kira Ararat wadanda an sami manyan tafkuna na ruwan
gishiri kuma ba sa gudana ko’ina. Manyan su ne tafkin Van da Urumiya. Samuwar
wadannan tafkuna ya dada tabbatar da ruwan dufana domin babu yadda za’a sami
tafkunan ruwan gishiri a lungunan da ba sa kusa da teku, sai dai idan bayan
ruwan dufana ne su ka samu sanadiyyar narkewar kankara.
Bayan wannan al’amari dabbobi da dama sun bace har abada sai dai
kawai kasusuwansu. Kuma an sami wasu sabbin jinsuna na dabbobi, don binciken
kimiyya ya tabbatar da cewa bayan ruwan dufana ne aka sami jakin dawa (Watakila
ratsa barbara cikin jirgin Nuhu). A cikin suratul Muminun Allah ya ce Q23:31
“Sannan kuma mu ka kaga wani karni, na wadansu mutane daban, da ga
bayansu” Bayan karewar mutanen Nuhu sai Allah ya ka ga
halittar wadansu mutane da su ke dabam da su.
Comments
Post a Comment