QUR’ANI DA KIMIYYA

 

Tsawon tarihin Dan Adam a doron kasa ya kasance mai fafutukar gano wanene shi, don me yake a nan duniya kuma shin menene makomarsa? Wadannan tambayoyi sun samo asali sakamakon nazarce-nazarce da shi Dan Adam yake yi a karan kansa da kuma dabbobin da suke kewaye da shi da kuma abubuwan halitta mara sa rai da ke sama da kasa. Wannan ya sa mutanen farko-farko suka kasance masu bautar abubuwan ban mamaki irinsu rana, taurari, hadari, tsawa dss wanda daga baya kuma sai aka rika sassaka gumaka domin su isar da bukatu ga ubangiji. Idan aka yi nazarin addinai masu bautar gumaka za a fahimci cewa suna amfani da gumakan ne a matsayin tsani zuwa ga ubangiji.

Abubuwa mafi tasiri a cikin tarihin Dan Adam tun farkon lokaci zuwa yanzu abu biyu ne; Wato Addini da Kimiyya. Duk da kasancewar wadannan abubuwa sun kasance hannun riga da juna amma sun fi komai tasiri cikin rayuwar mutane. A yanzu ina ganin mun kai matsayin da zamu fahimci rayuwa mu kuma amsa wadancan tambayoyi da aka yi shekaru aru-aru ana yin su. Dalili kuwa shine, ita dai Kimiyya aba ce wadda take zahiri, kuma karara yadda duk wanda ya bi tsarinta ko a Kano ko a Karachi zai same ta daidai wa daida. Sannan ita wannan kimiyyar muna iya amfani da ita wajen tabbatar da bayanai da addinai suka dade suna yi. Wasu na iya mamakin wannan bayani da tambayar ta yaya Kimiyya zata tabbatar da addini?

Idan dai har Allah shine ya halicci komai ya tsara su sannan kuma shine ya aiko da addini wajibi ne a samu Kimiyya cikin littattafan Allah. Domin dai mun fahimci cewa halittu, masu rai ko marasa rai ai dukkansu cikin wancan tsari na Kimiyya aka yi su. Abinda aka kasa fahimta shine cewa ita Kimiyya ba tsarin masananta ba ne, a’a domin kafin masana Kimiyya su wanzu aka samar da halittu masu rai da marasa rai kuma cikin tsari na Kimiyya. Idan mun fahimci haka sai mu gane cewa aikin masana Kimiyya bai wuce na gano yadda Allah ya tsara halitta ne kawai. Misali tun kafin a san za’a halicci mutum Allah ya halicci duniya kuma ya halicci lantar-maganadisu (electromagnetic waves) wadanda masana Kimiyya suka gano cewa ana iya sarrafa shi wajen aika sakonni na rediyo, talabijin, tangraho da kwamfuta.

Matsala tsakanin addini da Kimiyya matsala ce ta mabiya, wato masu addinai da masana Kimiyya, domin a bangaren masu addinai suna kallon masu Kimiyya a matsayin kafirai wadanda suka kore hannun Allah a halitta kuma suka yi watsi da duk wani abu wanda ba za a tantance shi  a yi nazarinsa a zahirance ba, misali maganar akwai Allah, mala’iku, wuta da aljanna. Wannan ya sa maimakon masu addini su banbance tsakanin Kimiyya da masananta sai suke gwamutsa su, don haka suka daura damarar yaki da kimiyyar.

Addini da Kimiyya tamkar gangar jiki ce da ruhi, wannan zahiri wancan badini, hadewar su wuri guda shike samar da cikkakkiyar halitta. Wajibi ne mun fahimci wannan auratayya wadda Allah da kansa ya kulla kuma musulmi ba zasu sami ci gaba na hakika ba har sai sun fahimci hakan kamar yadda magabatanmu na farko su ka yi. Wanda duk ke karanta tarihi, ya san cewa zakakuran malaman musulunci sun yi ja-gaba a fannoni na Kimiyya kamar su Al-Kwarizmi, Ibn Sina, Ibn Rushud da sauransu. Amma sai turawa suka karbe daga inda suka tsaya kuma suka habaka Kimiyya, a yayin da muke ta shirgar barci a yanzu.

A yau duniyar musulmi ta fada wani tarko da aka dana mana na ganin cewa mun yi watsi da hakikanin nazari na Qurani. Mun zama masu karatun aku kawai, wato mu koyi rera qira’a, mu karanta ayoyi cikin sAllah, mu koyi hadda da allo har da ma gasar cin kofi na duniya a Saudia, ba tare da mun yi nazari don fahintar sakonni na ilimai da ke tattare cikin littafin ba.

Kada mu manta Allah ya fara bamu sharadi na farko kamar haka

Q96:1 “Ka yi karatu da sunan ubangijinka, wanda ya yi halitta?

Karatu, kamar yadda na fada ba fa na aku ba, karatu na nazari na fahimtar ilimai. Wannan ne umarnin farko da aka ba Annabi domin kuwa Ilimi shine ginshikin rayuwar duniya, wanda duk yayi shi zai yi rayuwa mai kyau a nan kuma ya cimma tsira a lahira. Bayan wannan umarni sai me? Aya ta biyu da aka saukar wa manzon Allah ita ce ta Kimiyya

Q96:2 “Ya halitta mutum daga gudan jinni”

Wato Allah ya fara da bawa dan adam amsar da ya dade yana nema ta wanene shi? Idan yana son gane wanene shi dole sai ya fara da halittarsa, wato nazarin yadda aka halicce daga gudan jini. Wannan halitta tana daga cikin gagaruman hujjoji da idan mutum ya fahimce ta dole ya sallamawa ubangijinsa. Tun saukar da wannan aya shekaru 1400 babu wanda ya fahimci yadda wannan halitta take kamar mutanen zamaninmu. Domin har shekarun 1700 miladiya, mutanen duniya kaf na tsammanin ana haihuwar mutum ne sukutum yadda yake. Amma annabi yayi bayani cikin hadisi yadda daga maniyyi ake samin gudan jinni sannan tsoka. Bari mu bibiyi yadda ayoyin Qur’ani suka yi bayani tare da ilimin halittar jariri (embryology) da ilimin zahiri na Kimiyya ya tabbatar. Da farko Allah ya fara mana da cewa

Q36:36 “Tsarki ya tabbata ga wanda ya halitta nau’uka, namiji da mace, daga dukkan abinda kasa ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abinda ba su sani ba

Wato dukkan wata halitta, kama daga mutum, dabba, tsiro da ma abubuwan da bamu sani ba, sun kasance suna da nau’in mace da namiji. Ina hikimar haka? Na farko dai domin Allah ya tabbatar da cewa shi kadai ne tilo amma kowa na da mahadi. Sannan kuma it ace hanya guda ta wanzuwar jinsuna. Jima’I tsakanin mace da namiji shi ke samar da sabbin halittu. Amma kada mu dauka cewa muna da wani ikon domin Allah yayi mana gori cikin

Q56:58-59 “Shin, kuma kun ga abinda kuke fitarwa na maniyyi? Shin ku ne kuke halitta shi, ko kuwa mu ne masu halittawa?

Shi kansa kwayar maniyyi an halitta shi da wani tsari wanda yayi daidai da aikinsa domin yana nan kamar talibanban (yayan kwadi) yana da katon goshi da wani tsini a goshin da kuma jela wadda ke taimaka masa iyo. A yayin saduwa guda, namiji na fitar da a kalla kwayoyin maniyyi miliyan 8.3. Da zarar sun kwarara cikin farji sai su kama tsere a junansu su doshi mahaifa, kuma kalilan cikinsu ke kaiwa bakin mahaifar. Da isarsu sai a kama kokawa kowanne na kokarin fasa kewayen kwan mace ya fada ciki. Da zarar guda ya ci nasarar fasa kewayen, nan take sai ragowar su saduda su hakura. Wannan shine matakin halittar jariri na farko, wato auren maniyyi da kwai, ta hanyar dunkulewa su zama abu guda. Yayin wannan dunkulewa sai kwan mace ya kawo rabi na kwayoyin halittar gado (chromosomes) dake jikinsa shi ma maniyyi ya kawo nasa rabin. Wannan karo-karo da su ka yi sai ya samar wa jariri cikakkun kwayoyin halittar gado. Don haka ne kowanne jariri sai kaga ya gaji uwa ko uba ko yan uwan uba ko yaan uwan uwa ko kakanni ta wata siffa ko dabi’a. daga nan sai Allah ya ce

Q23:12 “Sannan muka sanya shi, digon maniyyi a cikin matabbata natsatstsiya”

Wancan dunkule yana shiga mahaifa sai ya dafe jikin bangon mahaifar. Wannan mahaifa na da rubin fatoci da ke tamkar filo ga jariri sannan ta cikinta yake ci da sha kuma ya fitsarar ya kasayar. Akwai nutsuwar da ta wuce wannan?

Q23:14 “Sannan muka halitta shi gudan jinni, sannan muka halitta gudan jinin tsoka”

Nan da nan sai jijiyoyin jini su kewaye wannan dunkule su kuma ratsa cikinsa ta ko’ina, wato ya zama gudan jini kenan. Jini zai fara kai iska da abinci cikinsa daga nan sai wannan dunkule ya fara hayayyafa ta hanyar rabewa gida biyu, biyun kuma ya rarrabu zuwa hudu, hudu zuwa takwas: haka dai haka dai har ya zama daruruwa ya zama tsokar nama. Cikin suratul Laili sai Allh yyi rantsuwa da

Q92:3 “Da abinda ya halitta namiji da mace”

Dan tayi na kasancewa mace ko namiji yayin da kwai da maniyyi ke bada karo-karo na kwayoyin halittar gado. A jinsin mutane, wadannan kwayoyin halittar gado guda 46 ne don haka yayin waccan dunkulewa sai kwai ya bada 23 maniyyi ya bada 23. A cikin kowanne 46 na mace ko namiji akwai guda biyu tagwaye wadanda ke da alhakin samar da jinsin mace ko namiji. A kwai suna kasancewa dogwaye guda biyu, amma a maniyyi suna kasancewa daya dogo daya gajere. Don haka yayin karo-karo idan na maniyyi ya bada dogonsa kaga zai hadu da guda na kwai wadanda dama duk dogwaye ne don haka duk sun zama dogwaye kenan wanda hakan zai sa jaririn ya kasance namiji. Amma idan ya kasance na maniyyin ya bada gajerensa wanda ya hadu da na kwai dogo, kaga zasu kasance dogo da gajere wanda sakamakon haka zai sa jariri ya kasance mace. A cikin suratul Hajj sai Allah y ace mana

Q22:5 “Sannan kuma (muka halitta ku) daga tsoka wadda ake halittawa da wadda ba’a halittawa”

Me Allah ke nufi da tsokar da ake halittawa da wadda ba’a halittawa? Tafsirin wannan aya ya ta’allaka ne idan ka kalli yadda dan tayi yake Rayuwa har zuwa haihuwa. Domin idan aka fito maka da dan tayi a matakai daban-daban alhalin baka san menene ba, zaka iya rantsewa ba zai yiwu a ce wannann ne ke zama mutum kamar ni da kai ba. Domin a satuttukan farko dan tayin yana kama da ‘ya’yan kwadi, sannan a wani lokacin yana da wasu tsagu a gefen inda kunne yake tamkar yadda na kifaye yake. Akwai lokacin da tsokokin wuya zuwa gadon baya suke tamkar na halittu masu rarrafe irinsu kadangare. Kai a takaice har doguwar jela yake da ita wadda sai kusan haihuwa sannan take zukewa. Wato a takaice tsokoki iri-iri wadanda a karshe ba’a halitta su. Daga karshe sai Allah ya ce mana

Q23:14 “Sannan muka halitta tsokar ta zama kasusuwa, sannan muka tufatar da kasusuwan da wani nama, sannan muka kaga shi wata halitta dabam. Saboda haka albarkun Allah sun bayyana, shine mafi kyaun masu halittawa”

Wato daga wani ruwa mai yauki, ya zama jini-jini sannan ya zama tsoka. Ita kanta tsokar aka dinga jujjuya ta tana daukar siffofi na dabbobi iri-iri sannan aka tsatso kashi daga cikin tsokar (wa iyazu billah) sannan aka maida tsoka da fata kan wannan kashi…wanene idan ba Allah ba ya isa yayi hakan? A takaice wannan ilimi na Kimiyya baifi shekaru hamsin ba a wajen masana Kimiyya amma yana cikin Qur’ani da hadisi tsawon shekara 1400. Dole ne mu fahimci cewa Kimiyya ba wani abu bace face tafsirin ayoyin Allah.

Comments

Popular posts from this blog

BAKAR TAURARUWA (BLACK HOLES)

RUKUNIN TAURARONMU-RANA

TSUNTSAYE