WUTA


Wuta, sinadari ce mafi mahimmanci a ginshikan samar da halittu da wanzuwarsu. Ba don wutar nan ba, da ni da kai da komai bai samu ba. Wuta  wata aba ce da ke samuwa sakamakon cudanyar kwayoyin zarra na iska da makamashi, haduwar wadannan kan haifar da zafi (heat) da kuma haske (light). A tarihin asalin halitta zamu ga cewa wuta ita ce ginshiki wajen canzawar kwayoyin zarra na farko mara sa rai. Kamar yadda muka gani cikin suratul fussilat Allah ya ce

Q41:11 “Sannan ya daidaita zuwa ga sama alhali kuwa ita (a lokacin) hayaki ce”

Allah ya fara kowacce halitta ne daga hayaki, wato wannan hayaki, binciken Kimiyya ya gano cewa shine hayaki mafi tsufa wato hayakin hydrogen (jinsin kwayoyin zarra na farko) domin ita ke da kashi 90% na yawan kwayoyin zarra a sammai da kassai. Wannan hayaki ya sami damar samar da halittun farko na taurari sakamakon dunkulewa waje guda a farkon lokacin halitta. Allah ya ce mana cikin Sutatul Anbiya

Q21:30 “Shin wadanda suka kafirta ba su gani cewa lallai sammai da kasa sun kasance a dunkule (waje guda) kafin mu tarwatsa su?”

Wato tsananin takura waje guda na kwayoyin zarra cikin wannan hayaki sai ya haifar da zafi wanda ya sa suka fara konewa har ta kai inda suka tarwatse, tarwatsewa irin ta nukiliya. Wannan tarwatsewa ita ce haihuwar wannan sammai da kassai (Big Bang). Taurari sun samu ne sakamakon  maganadisu na tattara sassa na hayakin da ya tarwatse. A duk lokacin da maganadisu ya tattaro wani kaso waje guda sai kwayoyin zarra na wannan sashe su fara konewa, wadda ke haifar da zafi da kuma haske. 

Har yanzu duk ilahirin taurarin da muke hange a sararin samaniya, ba komai bane illa dunkulen hayaki wanda kwayoyin zarra da ke ciki ke konewa. Taurari tamkar sauran halittu suke wato dai ana haihuwarsu, su tsufa kuma su mutu. Haihuwarsu ita ce lokacin da maganadisu ya tattaro tuttukar hayaki kuma kwayoyin zarra dake ciki suka fara konewa don samar da haske da zafi. Iyakar yawan kwayoyin zarra da ke cikin wannan hayaki da kuma iyakar saurin konewarsu, shi ke nuna tsawon shekarun da zasu yi a raye suna bada haske da zafi. Karshen rayuwar taurari kuwa na kasancewa dayan hudun nan

-Wani tauraron a yayin da yazo karshen rayuwarsa, wato lokacin da ya kusa kone duk kwayoyin zarra da ke cikinsa sai ya tarwatse, tuttukar hayakin ta barbaje zuwa sassa. Wannan tuttuka ita ke sake zama wasu sabbin taurarin a duk lokacin da maganadisu ya sake tattaro su wuri guda ko kuma idan sun daskare sai su samar da duniyoyi  (Su masana ke kira da Nebulae).

-Akwai kuma wasu taurarin da idan suka gama kone kwayoyin zarra da ke cikinsu sai su kasance sun gaza fitar da haske da zafi, wato su yi sanyi kuma su dusashe. Wadannan taurari sun mutu kurmus kenan (Su ake kira da White dwarf)

-Wasu kuma idan sun kai wani zango na rayuwarsu sai su takure su yi wata irin matsananciyar dunkulewa. Saboda tsananin karfin maganadisun su a wannan yanayi, hatta hasken su baya iya fita daga tauraron don haka duk da cewa suna nan ba a iya ganinsu. Masana na gane su ne kawai ta hanyar kula da tasirinsu a kan taurari da ke makwabtaka da su, domin za’a ga suna zuke hayakin wadannan makwabta nasu. Kuma duk wani abu da ya gitta ta kusa da su sai su lakwume shi (Wadannan su ake kira da bakar tauraruwa wato Black holes)

-Na karshe sune taurarin da suma ke irin waccan dunkulewa amma kuma maganadisun su baya takurewa yadda zai iya hana haske fita, amma saboda dunkulewa waje guda sai haskensu ya ninninka. Su ake kira da dunkulalliyar tauraruwa (Wato Neutron star)

Don haka duk taurari wuta ce mai tsananin zafi, wadda zafin ta baya misaltuwa. Idan ka dauki tauraron mu, wato Rana, zafin cikinta yana farawa daga kimanin Degree 12,000 a ma’aunin zafi na centigrade (Ka kwatanta zafin da na tafasasshen ruwa wanda degree 100 ne kawai). Da za’a iya ciro wani bangare na rana daidai da girman kan allura, a ajiye shi a Zaria zai iya kone mutumin da yake Kano. Wasu taurarin sun fi wasu tsawon rai, wanda hakan ya ta’allaka ne da nauyin kwayoyin zarra da ke cikinsu, akwai wadanda ke shekaru Biliyan 5 zuwa sama kafin su mutu. Misali namu tauraron, wato rana, wadda a yanzu shekarunta ya kai kimanin shekara bilyan 4.6, nan gaba kuma zata iya kai wasu shekaru biliyan 7 kafin kwayoyin zarra da ke cikinta su kone kurmus.

Rana ginshikin rayuwarmu ce a wannan duniya, idan babu ita ba wata halitta da zata iya Rayuwa a doron kasa. Allah ya fada mana ayyukan rana cikin Qur’ani a wurare daban-daban. Misali

Q24:44 “Allah yana juyar da dare da yini. Lallai cikin wannan akwai abin kula ga ma’abuta idanuwa”

Juyawar kwallon duniya daga gabas zuwa yamma shike samar mana da sabanin dare da yini, kuma wannan wani babban ginshiki ne na wanzuwar Rayuwa a doron duniya. Kamar yadda na fada a baya zafin rana ya fara ne daga degree 12,000 a farfajiyar samanta wanda ke karuwa da nutso cikin rana. Wannan zafi na isowa doron duniya bayan yayi tafiyar kilomita miliyan 150. A daidai wannan zangon shine rana ba zata iya yi mana mummunar illa ba, domin akwai Karin matakai da Allah ya halitta da ke rage shi kansa wannan zafi. Na farko dai kasancewar duniya na juyawa, kuma ba don wannan juyi ba idan aka ce rana jiddin muke fuskantarta, cikin yan kwanaki komai a doron kasa zai kone kurmus. Sannan da a ce jiddin a cikin dare muke, shima cikin yan kwanaki komai zai daskare saboda sanyi. Amma wanna juyi sai ya daidaita lamarin yadda kafin zafi ya wuce kima sai dare ya shigo ya sanyaya mu. Haka nan kasancewar duniya na juyawa a cikin awa ashirin da hudu an sami tsawon yini da dare sun raba daidai (awa 12) face a doron duniya na yamma da gabas inda lokacin sanyi ake samu yini na awa shida kacal tsawon wata shida ko kuma a lokacin zafi ake samun dare na awa shida shima. Wannan ya bamu yanayi mai nutsuwa da zamu iya Rayuwa, wato bamu kusanci rana yadda zamu kone ba kuma bamu nisance ta yadda zamu daskare ba. Idan muka dubi duniyoyi da ke makwabtaka da mu, wadanda suka fi kusanci da rana, wato kamar mercury, wadda ke da tsawon yini guda daidai da watanni uku na duniyar mu, zafin  rana ya kan kai degree 800 a ma’aunin zafi (misalin tafasashshen ruwa sau takwas). Sannan idan dare yayi ta na hucewa zuwa kimanin kasa da -300 a ma’aunin sanyi (wato kamar sanyin kankara ka ninka shi sau 75 kenan). Idan ka kwatanta da zafin da ya fi kowanne da aka taba samu a duniya shine degree 101 cikin saharar Libya sannan sanyi mafi tsanani ya faru ne a hamadar kankara da ke Siberia wato kimanin kasa da -95. A wannan duniya ta mercury babu wata halitta da ke doron kasa da zata iya Rayuwa don ko karfe ka ajiye a kanta zai yi laushi saboda zafi.

Q10:5 “Shine wanda ya sanya muku rana, babban haske”

Wani daga cikin ginshikin aikin rana shine na samar da haske, wannan haske yana tallafar rayuwarmu domin da shine dukkan tsirrai ke iya Rayuwa ta hanyar sarrafa taki da ruwa da abincin da suka ci domin su girma, mu kuma mu cinye tsirrai don mu rayu. Abubuwan da rana ke mana yana da yawa, kuma kamar yadda da ita Allah ya tsara yadda zamu rayu, haka nan da ita Allah zai halakar da mu a karshen zamani kamar yadda ya bamu labari cikin

Q75:6-9 “Yana tambaya “yaushe ne ranar kiyama? (kace) idan gani ya dimauta (yayi kyalli) kuma wata yayi husufi (hakensa ya dusashe). Aka tara rana da wata (waje guda)”

Cikin layi biyu zuwa uku Allah ya gaya mana yadda duniya zata tashi. Wato a lokacin da rana ta kone mafi yawan kwayoyin zarra da ke cikinta sai ta kumbura ta kuma watso hayakin da ke kewaye da tsakiyarta. Wannan lamari zai sa haskenta ya ninninka sau daruruwa (wato idan akwai masu kallo a lokacin hakika ganinsu zai dimauce da kyallinta kamar yadda ayar ta ce). Sannan wannan hayaki da ta watso mai tsananin zafi zai kone ilahirin duniyoyin da ke kusa da ita, har da duniyarmu da watanmu. Kaga a wannan lokaci wata zai daina bada haske domin rana ta lankwame shi, ya zama ya fada cikin rana kenan kamar yadda ayar ta ce “Aka tara rana da wata”.

 

 

Comments

Popular posts from this blog

BAKAR TAURARUWA (BLACK HOLES)

RUKUNIN TAURARONMU-RANA

TSUNTSAYE