BULAGURO A SAMA’U
Ranar 5 ga watan Satumba na shekarar 1977, daga filin tasar
jiragen Roka da ke Cape Carnaveral a kasar Amurka aka harba jirgin Voyager 1
domin nausawa cikin sama’u ya samo mana bayanai da hotuna yadda rukunin wannan
tauraro namu, wato rana ya ke. Shugaban wannan shiri shine shahararren masanin
ilimin sararin samaniya, wato Carl Sagan, wanda ya sa aka nadi sautukan
muryoyin gaisuwa a yaruka 54 da ke duniya da nufin ko da wannan jirgi zai hadu
da wasu halittun da ke cikin sammai. A satin da ya gabata ne wannan jirgi ya
kai nisan zangon adadin kilomitar sammai 150 a yayin da ya shekara 43 ya na
tafiya ba kakkautawa, a gudun da ya kai kimanin kilomita dubu sittin a awa
guda. Ita kilomitar sammai guda daya nisanta shine kwatankwacin nisan wannan
duniya tamu izuwa rana wanda a kilomitar duniya miliyan 150 ce. Saboda girma da
fadin sammai ya sa sai da irin wannan awo za’a fahimci nisan wurare a sama’u.
Idan mu ka lissafa wannan nisa da Voyager ya kai a yanzu, wato kilomitar sammai
150, a kwatankwacin kilomita a duniya, ya kama kilomita biliyan 22.5 ke nan.
Idan zaka zagaya wannan duniya tamu nisanta bai wuce kilomita dubu arba’in ba
(sai ka kwatanta sau nawa zaka zagaya duniya kafin ka kai nisan kilomita
biliyan 22.5 inda Voyage ya ke a yanzu? Wato sai ka zaga duniya sau 562,500
kenan).
A iya wannan gudu da jirgin Voyager ke tafiya na kilomita
60,000, zai dauke shi shekaru 300 nan gaba kafin ya kai hadarin Oort, shi
hadarin Oort wani dandazo ne na duwatsu da kankara wanda ya ke tamkar bango na
iyakar rukunin tauraron mu, wato rana. Kana wuce hadarin Oort ka fita daga
rukunin tauraronmu wanda ke kunshe da duniyoyi 8 (Solar System). Shi wannan
rukuni namu ya na gefe ne a wannan dabaka tamu wadda ake kira da milky way,
nisansa zuwa tsakiyar wannan dabaka ta milky tafiyar da haske zai yi ce ta
kimanin shekaru 27,000. Saboda tsananin nisa tsakanin dabakoki, ma’aunin da ake
amfani da shi ya fi karfin kilomitar sammai wadda ta ke kilomita miliyan dari
da hamsin ce kacal, don haka sai ake amfani da abinda ya fi komai sauri a cikin
halittun ubangiji na zahiri, wannan shine haske. Haske ya na da saurin kilomita
186,000 a sakan guda ko muce kilomita tiriliyan 9.4 ashekara. Don haka jirgin
Voyager sai ya yi tafiyar kilomitar sammai sau dubu 63,239 kafin ya iya yin
tafiyar da haske zai yi a shekara guda. Wato yin wannan tafiya ta kilomitar
sammai dubu 63,239 zai dauki Voyager kimanin shekaru 67,455 kenan kafin ya yi
tafiyar haske ta shekara guda. Tauraro mafi kusanci da Rana shine tauraron
Proxima Centauri, wanda ke da nisan tafiyar haske ta shekaru hudu, kada mu
manta cewa a wannan Dabaka ta mu ta Milky Way, akwai kimanin taurari dai-dai
har biliyan 400, amma Proxima Centauri ce makwabciyar mu mafi kusa kuma nisanta
ya kai tafiyar haske ta shekara hudu. To mu dauka Voyager 1 zai doshi wannan
tauraruwa, sai ya shafe shekaru 269,820 kafin ya isa kenan. Fadin wannan Dabaka
ta Milky Way daga gaba zuwa gaba kuwa, tafiyar haske c eta shekaru 100,000.
Idan mu ka ce jirgin Voyager zai ratsa fadin dabakar mu kuwa zai dauke shi
shekaru biliyan 6.7 kenan, tsawon shekarun da sun girmin wannan duniya tamu
wadda bat a wuce shekaru biliyan biyar ba. Wannan fa a Dabaka guda daya kawai
mu ke tafiya kuma akwai Dabakoki irin Milky Way sama da Tiriliyan biyu a
warwatse cikin sama’u. Har yanzu ka na jin cewa mun kai digon allura a cikin
fadin wannan sammai?
A yanzu a iya ci gabanmu na fasahar kera jirage masu tafiya
cikin sammai, idan jirgin namu na Voyager zamu tura shi Dabaka mafi kusa da
tamu, wato Dabakar Andromeda wadda ked a nisan tafiyar haske ta shekaru miliyan
biyu, sai nan da shekaru biliyan 126 masu zuwa jirgin zai isa. Ita kanta wanna
sammai ta mu daga lokacin da Allah ya faro halittar ta, sakamakon haske mafi
tsufa da muka iya gani ya tabbatar da cewa bat a wuce shekaru biliyan 13.8 da
samuwa ba, kaga tafiyar Voyager zuwa Dabaka mafi kusa da mu za ta ninka tsawon shekarun
sammai da kassai kusan sau tara kenan. Hatta hasken wannan Dabaka na Andromeda
da mu ke gani a yanzu ya shekara miliyan biyu yana tafiya kafin ya iso mana
kuma hasken day a baro ta a yanzu da na ke wannan rubutu ba zai iso nan ba, duk
da gudun day a ke ni kilomita 186,000 a sakan guda, sai nan da wasu shekaru
miliyan biyu masu zuwa. Ya ilahi ina maganar sauran dabakokin Tiriliyan biyu,
zancen ka liddafa su kaga bai ma taso ba. To duk wannan ba shine mafia bin
mamaki ba sai fadar Allah cewa
Q37:6 “Lallai mu, mun kawatar da sama ta kusa da wata kawa,
watau taurari”
Subhanallah! Ba zaka fahimci wannan bayani a zahiri ba sai ka
fahimci ilimin sararin samaniya na zamani. Domin muna maganar cewa zancen
lissafa nisan zuwa dabakoki Tiriliyan biyu bai ma taso ba, to sai gas hi Allah
n ace mana dukkan wadannan taurari a cikin dandazonsu na dabakoki kimanin
tiriliyan biyu da muke iya hangowa (abinda masana ke kira da Observable
Universe) dukkansu a sama ta kusa su ke. Waccece sama ta kusa? Sai Allah y ace
cikin Surar Mulki
Q67:3 “Shibe wanda ya halitta sammai bakwai, dabakoki a kan
juna, ba za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) MAI Rahama. Ka sake
dubawa ko za ka ga wata Baraka?”
Wato duk wadannan Dabakoki Tiriliyan biyu da muke iya hangowa a
sama ta daya kawai su ke cikin sammai bakwai, it ace waccan sama ta kusa da
Allah ya ambata. A bayyane yak e cewa duk iya ci gaban da Dan Adam zai cimma a
kere-kere na jirage ba zamu iya ratsa dabakar mu ta milky way ballantana saura
dabakoki tiriliyan biyu. Kai hatta maduban hangen nesa da mu ked a su wadanda
gannannmu ke iya hango fadin sama’u (a yanzu muna da madubin Hubble wanda aka
harba sararin samaniya day a bamu ikon gane cewa akwai dabakoki kimanin
tiriliyan biyu a sama’u) shi kansa wannan madubi baya iya hango dabakokin das u
ka kai nisan tafiyar haske ta shekaru biliyan 42. Dalili kuwa shine Allah y ace
mana
Q51:47 “Kuma sama mun gina tad a wani irin karfi, alhali kuwa
lalle mu ne masau fadada ta”
Karfin magandisu (gravity) shine ginshikin samuwa da wanzuwar
halittun sammai. Magandisu ya baiwa duniya ikon kewaya rana, ita kuma rana ke
kewaya dabakar milky way wadda ke kewaya dandazon dabakoki. Tun da Allah ya
samar da sammai daga wani dunkule wadda ya bayyana a cikin suratul Anbiya
Q21:30 “Shin kuma wadanda su ka kafirta bas u gani cewa sammai
da kasa sun kasance a dunkule sannan muka tarwatsa su?”
Wannan shine bayanin dam asana sararin samaniya su ka gano na
Big Bang shekaru kusan dari das u ka wuce, wanda hujjojin kimiyya su ka
tabbatar das hi a matsayin samuwar wannan sammai kuma ta k eta fadada
bangarorin gabas da yamma, kudu da arewa, har zuwa yanzu kuma ta ke ci gaba da
fadada. Wannan fadada ita ta sa hatta dabakokin dake cikin wannan sammai tamu
idan sun kai nisan tafiyar haske na shekaru biliyan 42 ba zamu iya sake
ganinsu. Wannan ya zamar mana bango na iya inda zamu iya kalla a fadin sammai,
wato sama ta daya. Haka nan kimiyya ta tabbatar da cewa taurari da dandazon
dabakokinsu gaba daya da ke cikin sammai su ne kaso 4.9% kacal na halitta.
Ragowar kaso 95.1% ya kasance cikin halittar da ba’a iya gani (Dark Matter
wadda ked a kaso 26.8%) sai kuma kuzari da ba’a iya gani (Dark Energy wanda ked
a kaso 68.3%). Shin a cikin tsarin halittu, idan ka yi la’akari da wadannan
bayanai, mun kai kwatatnkwacin digon allura a teku?
Shi ya sa Allah ya ce mana
Q79:27 "Shin ku
ne mafi wuyar halitta ko sama” Allah ne ya gina ta?"
Comments
Post a Comment