DAIDAITO CIKIN SAMMAI DA KASSAI

 

Q13:2 “Allah shine wanda ya daukaka sammai ba da ginshiki wanda ku ke iya gani ba. Sannan kuma ya daidaita a kan Al’arshi, kuma ya hore rana da wata, kowanne ya na gudana zuwa ga ajali ambatacce. Ya na shirya al’amari, ya na rarrabe ayoyi daki-daki, mai yiwuwa ne ku yi yakini da haduwa da Ubangijinku”

Allah ya halicci wannan sammai da kassai da muke ciki bisa doron wani cikakken tsari mai daidaito wanda idan da a ce zai kauce daidai da kwayar zarra ko akasin haka da sammai ba ta wanzu ba balle ta habaka. Kamar yadda Allah ya fada a aya ta sama ba ma iya ganin ginshikan da ke dauke da sammai da kassai, amma binciken kimiyya ya gano cewa wannan sammai ta samo asali daga wata gagarumar tarwatsewar ta wani karamin dunkule wanda ya haifar da wannan sammai da kassai da mu ke ciki

Q21:30 “Shin wadanda ba su yi imani ba, ba sa ganin cewa sammai da kasa sun kasance a dinke waje guda kafin mu tarwatsa su?”

Wannan tarwatsewa ta nukilya ita ta watsa kwayoyin zarra masu tsananin zafi a guje zuwa sassa na gabas da yamma, kudu da arewa a fadin wannan sammai. Daidaiton karfin gudun da kwayoyin zarra su ka zabura, na kan wani mizani kayyadadde wanda da ya gaza daidai da kashi daya cikin adadin miliyan dubu sau dubu sau dubu (wato jumla mai sifili 60 kenan) ko a saukake mu ce daya cikin malala gashin tinkiya, to da wannan yaduwa ta kwayoyin zarra ba za ta iya ci gaba ba yadda har za’a sami taurari da duniyoyi, sannan da kwayoyin zarrar sun koma sun sake dunkulewa. Haka nan da zaburar ta wuce wannan adadi daidai da kashi daya cikin waccan jumla, hakika da kwayoyin zarra sun daidaice yadda ba za su iya dunkulewa yadda za su samar da taurari da duniyoyi ba.

Akwai abubuwa guda hudu wadanda su ne turaku na wanzuwar wannan sammai da kassai. Na farko shine nukiliya mai karfi (strong nuclear force) wanda shi ne ke baiwa kwayar zarra damar kasancewa dunkule waje guda yadda ba ta tarwatse ba. Sannan akwai nukiliya mara karfi (weak nuclear force) wanda shi kuma ke baiwa kwayoyin zarra damar rubewa. Akwai lantarmaganadisu (electromagnetism), wanda shine ke samar da sararin da lantarki da maganadisu ke iya tafiya ciki sannan a karshe akwai karfin maganadisu (gravity) da ke baiwa abubuwa nauyinsu da kuma damar cudanya da juna. Kowanne cikin wadannan abubuwa su na kan tsarin daidaito da bai yi yawa ko ya gaza ba, domin duk wanda a cikinsu ya gaza ko yayi yawa, to rayuwar sammai da kassai yadda a ka sani ba za ta yiwu ba.

Kwayar zarra ta farko da Allah ya halitta ita ce ta hayakin Hydrogen, wadda ita ce tamkar Adam a mutane, domin duk wata kwayar zarra daga ita ta samo asali. Ita ce kenan ginshikin samuwar sammai da kassai da kuma asalin yadda rayuwa mai rai ta samo asali, domin dai da ita da kwayar zarrar Oxygen ne su ke haduwa domin samar da ruwa. Kowacce halitta mai rai a doron kasa ta samo asali daga ruwa kamar yadda Allah ya sanar da mu cikin

21:30 “..Kuma mu ka sanya kowacce halitta mai rai daga ruwa”

Misalin tasirin turakan samar da wanzuwar sammai shine idan da ace an sami rashin daidaito tsakanin nukiliya mara karfi da kuma karfin magandisu, to da duk kwayar zarra ta Hydrogen zata canza ta zama Helium (wato Hawwa’u kenan a halittu marasa rai). Idan kuma da ace nukiliya mai karfi ya gaza ko yaya, to da duk sauran kwayoyin zarra banda Hydrogen da ba su samu ba, wato da rana da taurari da duniyoyi da ni da kai duk ba mu samu ba.

A wani bangaren kuma, idan da a ce lantarmagandisu ya yi karfi fiye da yadda ya ke, yayan kwayoyin zarra (electrons) za su damfare yadda ba za su iya cudanya da juna ba yadda za’a iya samar da dunkulewar kwayoyin zarra zuwa azuzuwa (chemical compounds), sannan kuma da lantarmaganadisun ya yi rauni a kan yadda ya ke, shi ma da sai kwayoyin zarra su rika saurin rubewa cikin dan kankanen lokaci kafin su dunkule. Daidaiton kwayar zarrar Carbon, wadda ita ce ginshikin yin jukuna na abubuwa masu rai da marasa rai, da shi ma ya yi kasa da kashi 4% kacal a kan yadda ya ke da manyan kwayoyin zarra da ake samarwa daga rushin cikin taurari da ba su samu ba, kun ga da babu rayuwa kenan.

Duk da kokarin masana kimiyya na yadda su ka gano yadda sammai da kassai su ka faro daga tarwatsewar nukiliya a farkon lokaci, binciken su ya ci karo da bangon karfe da su ka kasa iya wucewa. Waton duk abinda ya faru kafin dakikoki 43 bayan wannan tarwatsewa, babu abinda a ke iya fahimta. Wato iliminmu ya takaita daga wannan lokaci, domin duk lissafin da za’a yi ba a iya wuce wannan lokaci, don haka ba wanda ya san me ya faru kafin dakika 43 bayan tarwatsewar, sai dai a yi hasashe kawai. Dalili kuwa shine a wanann lokacin, saboda kankanta da zafi na jaririyar sammai da kassai, ya hana a gane ya maganadisu (gravity) ke iya ta’ammali da kananan yayan kwayar zarra (quantum world). Masana kimiyya sun dukufa wajen lalubo hanyar da za su iya fahimtar wannan yanayi na jaririyar sammai da kassai mai tsananin kankanta da yadda maganadisu ke ta’ammali da ita amma sun gaza gane komai kawo yanzu, sai dai watakila nan gaba Allah ya iya hore mana wannan ilimi ko kuma zai kasance kamar yadda dokar tsarin rashin tabbas (Uncertainty principle) wadda masanin kimiyya Heisenberg ya gano na cewa duk yadda mu ka so ba zamu iya a lokaci guda gane sauri (velocity) na yayan kwayar zarra (electrons) da kuma inda su ke (position) a cikin kwayar zarra ba. Wannan yanayi ba ya samu sakamakon rashin kayan awo ba ne na kimiyya, a’a tsari ne na yadda Allah ya tsara wadannan yayan kwayoyin zarra na yadda sai dai ka iya auna saurinsu ko ka iya gano inda su ke daban daban amma ba duk biyun a lokaci guda ba. Wannan tsari na rashin tabbas (uncertainty principle) ita ce kadai wata doka a kimiyya wadda duk wani bincike ya tabbatar da tabbacinta.

Don haka duk wadanda ke cewa idan aka bibiyi komai sannu a hankali za’a iya tarar da asalinsa, abinda dokar rashin tabbas ta kimiyya (uncertainty principle) ta kimiyya ta rushe wannan tunani. Wannan sammai ta mu ta faro kimanin shekaru biliyan goma 14-15 kuma tun daga sannan ta ke ta fadada cikin sauri ta na samar da halittu iri-iri. Hujjojin kimiyya sun tabbatar da cewa an fara samar da kwayoyin zarra kimanin shekaru 5000 bayan tarwatsewar farko, sannan sun fara cakuda da juna a wajajen shekaru 400,000, amma sai bayan shekaru kimanin miliyan 700 sannan aka fara samun dabakoki (galaxies) wanda daga baya kuma a kimanin shekaru biliyan 8 sannan aka sami duniyar mu wadda ita kuma sai da ta shekara biliyan 3 sannan a ka fara samun halittu masu rai. A yanzu a iya binciken kimiyya ya nuna cewa kasafin sammai da kassai ya kasance kashi 73% kuzari ne mai duhu (Dark energy) sannan kashi 23% kuma kwayoyin zarra ne masu duhu da ba’a iya gani (Dark matter) sai ragowar kaso 4% kacal na kwayoyin zarra wadanda a ke iya gani da su ka yi taurari, duniyoyi da ni da ku.

A yanzu a cikin iya inda maduban duba sararin samaniya (Telescopes) wadanda mu ka kera ke iya hanga (observable universe), akwai kimanin dabakoki (galaxies) tiriliyan biyu. Dabakar mu (Milky Way) ta na da fadin da ya kai kimanin nisan tafiyar haske ta shekaru 100,000. A cikin wannan dabaka tamu akwai taurari irin ranar mu kimanin biliyan 400. Tauraron da ya fi kusa damu, wato Proxima Centauri ya na da nisan tafiyar haske ta shekaru 4 kacal daga inda ranar mu ta ke. A yanzu yadda muka tura jirgin Voyager wanda ke tafiyar kilomita 60,000 a awa guda, zai dauke shi shekaru 139,000 kafin ya je tauraro mafi kusa da mu. Kada mu manta fadin dabakar mu kuma tafiyar haske ce ta shekaru 100,000. Sannan dabaka mafi kusa da mu ita ce ta Andromeda Galaxy, wadda idan ka fita daga dabakarmu ta Milky way ka doshe ta a gudun haske, sai kayi shekaru miliyan 2 sannan za ka isa can. Kuma akwai dabaka-dabaka irin tamu ta Milky way da ta Andromeda guda tiriliyan 2 a sammai wadda mu ke iya gani. Wanann sammai da mu ke iya gani (Observable Universe) wadda ke kunshe da dabakoki kimanin tirilayan 2, ita ce kaso 4% kacal na yawan abubwan da ke cikin sammai da kassai. A takaice wannan na nuna mana cewa cewar mu ba mu kai kwatankwacin digon Allura a cikin teku ba, kamar yadda Allah ke tabbatar mana cikin

Q79:27"Shin ku ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah ne ya gina ta. Ya daukaka rufinta sannan ya daidaita ta. Kuma ya sanya duhunta da kuma haskenta. Kuma kasa a bayan haka ya mulmula ta. Ya fitar da ruwanta da makiyayarta"

Allah shine ya tsara komai kuma ya saka wasu shingaye da duk yadda mu ka kai da ilimi ba za mu iya tsallake su ba. Cikin wadannan shingaye akwai, yadda sammai ta faro daga tushen asali, yadda rai ya ke samuwa, iya tantance sauri da inda yayan kwazar su ke da kuma hana mai rai ya mutu. Allah ya tsara halittarsa kuma ya saka wasu ginshikai da ba ma iya gani da ke dauke da wannan sammai da kassai, cikin wadannan ginshikai ya sanar da mu wasu wasu kuma ya boye mana su har abada, domin ya tabbatar mana da cewa shi kadai ne mahalicci kuma ya na sane da duk abubuwan da ya halitta kama daga mafi kankantar yayan kwayar zarra zuwa mafi girman dandanzon dabakoki.

Wajibi mu fahimci cewa babu yadda za’ayi wannan tsari mai cikakkiyar ka’ida wanda ko yaya aka motsa shi, wannan sammai ba za ta iya samuwa ba, sannan wani maras tunani da sunan kimiyya ya ce mana ita ta samar da kanta. Shin akwai wani abu a kimiyance da zamu iya nunawa mu ce ya samar da kansa ba tare da kowacce irin sila ba? Duk wanda ke son mu kore samuwar Allah to kalubalensa shine ya samar mana da kwayar zarra da kansa kuma ba tare da ya yi amfani da wata sila ta ubangiji ba. Idan sun kasa yin haka, kuma tabbas ba za su iya ba, to wajibi mu sallamawa fadar Allah cewa

Q72:28 “..Kuma shi Ubangiji ya kewaye su da sani, kuma ya lissafe dukkan komai da kididdiga”

 

Comments

Popular posts from this blog

HUJJOJIN TASHIN KIYAMA A KIMIYANCE

RUWAN DUFANA

QUR’ANI DA KIMIYYA