GANGAR JIKIN DAN ADAM


Allah ya ce mana cikin suratul Tin 95:4 “lalle mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa” A halittun duniya babu wanda ya kai Dan Adam kyawon siffa sannan jikinsa yafi kowanne irin mashin da ka sani.

Akwai yan rahoto (Receptors) miliyan hudu warwatse jikin fatarmu da ke banbance mana zafi, sanyi, tabawa ko ciwo. Fatarmu an yi ta rubi biyu don kare jiki daga bushewa da kuma adana ruwa da ke cikin jiki. Tana mana kariya daga sinadarai masu guba da kuma yanayi na sanyi ko zafi ta hanyar daidaita dumin jikinmu (temperature). A cikin bakin mu kan harshe, akwai kananan hudoji guda dubu tara wadanda ke taimaka mana banbance dandanon zaki, gishiri, tsami da sauransu. Jikin mutum na dauke da silin gashi miliyan biyar, wanda kowanne na iya Rayuwa ta akalla shekara 7. Wannan gashi, idan banda ta hanyar konewa, yana da wahala a iya lalata shi ta hanyar danshi ko ruwa ko amfani da wasu sinadarai. Kowanne sashe na jiki dandazon kwayoyin halitta (Cells) ne ya samar da shi, kuma cikin kowacce kwayar halitta akwai kwayar halittar gado (Genes), wdadda Dan Adam yana da akalla wadannan kwayoyi na genes guda 25,000, wadanda ke sarrafa komai da ke faruwa cikin jiki. Cikin ayyukansu shi ne sabunta halitta da kulawa da daidaiton tsare-tsaren da ke dauke da halitta. Wadannan kwayar halittar gado su ke dauke da kamanni na zahiri, kamar su launi, kauri, tsawo, fadin fuska d.s.s. A badini kuma su ke kula da dabi’a da kuma ayyukan abubuwa da mutum bashi da iko a kan su, irinsu ‘yan kanzagin jiki (Hormones) ta hanyar ba su umarni inda zasu je suyi aiki. Yan kanzagi su ke kula da misali, a wajen jiki, yadda yawu ke zuba ko nono ko kuma maniyyi. A can cikin jiki kuma su ke kula da zubar sinadarai cikin jiki domin su sanar da wani bangare abinda wani sashe ke bukata ko kuma ya yi yawa don a tsai da shi (misali zubar sinadarin da ke sanar da jin tsoro, jin yunwa d.s.s.). Jini kuma shi ke dakon iska, abinci da magani zuwa sassa da ke bukatarsu.  A cikin jini akwai wasu sojoji (Antibodies) wadanda ke yakar cututtuka da duk wani abu bako da ya shigo kuma jiki bai yarda da shi ba. Su kan yi gangamin yaki su far ma wannan abu har sai sun murkushe shi. A duk sa’a guda, Zuciya na burtso kusan galan biyu da rabi na jini ta hanyoyin jijiyoyi, wadanda da za’a jona kowacce jijiya da yar uwarta a mike su, tsawon su zai kai kimanin kilomita dubu 96,000 (Kusan kewaya duniya sau hudu kenan). A cikin jinin dai, akwai kimanin kwayoyin jini (jajaye) kusan tiriliyon 25 wadanda su ke dakon iska. Duk da wannan yawa nasu, kowanne guda daya baya wuce wata hudu suke mutuwa. Su kuma kwayoyin jinni wadanda ke yakar cututtuka, akwai kimanin kwaya biliyan 25 wanda basa wuce  awa goma sha biyu.  A kan haifi jariri da kimanin kasusuwa 305 amma idan yana girma wasu na hadewa har sai sun dawo 206 wadanda tsokoki da kwanji 650 ke sarrafawa tare da gabobi 100. Duk wadannan abubuwa tare da ayyukansu, su na samun umarni ne da ga hedkwata wato kwakwalwa, wadda ke sarrafa duk wani abu da ke faruwa a cikin jiki wanda muke sane da ma wanda ba mu sani ba. Kwakwalwa saboda mahimmancin ta a Rayuwa, ita ke da rabin kaso na kwayoyin halittar gado (wato kusan dubu 13,000 daga dubu 25,000 da mutum ke da su). Kwakwalwar mutum na da kwayoyin halitta da ke daukar sako (Neurons) daga kwakwalwa zuwa sassan jiki, kimanin biliyan 100 wanda ke da joni da juna kusan tiriliyon daya.Wannan sako yana ratsawa ta hannun masu mika shi (synapses) wanda ke da saurin da za a kwatanta da gudun mita 100 a sakan guda. Lantarkin cikin kwakwalwa shine ke baiwa wadannan halittu kuzarin gudanar da ayyukansu. A takaice kwakwalwa na aika sakonni miliyoyin a cikin dakika daya. Kowacce halitta mai rai na da kwakwalwa, idan ka dauko da ga kwayar halitta (cell) za ka fahimci komai nata a ka’idance yake yadda za ta yi rayuwarta. Su kuma manyan halittu, da ke da miliyoyin kwayoyin halitta, akwai tsari na ka’ida  da kwayoyin halittarsu ke bi ba tare da hargitsewa ba. Idan kayi tsani na halittu bisa la’akari da girman kwakwalwa za ka tarar cewa mutum shi ne a kokoluwar tsanin. A halittu idan ka duba mafi basira, irinsu kare da biri da wasu kifaye, zaka samu girman kwakwalwarsu baya wuce 650 cc amma mutum girman kwakwalwarsa ya kai 1450 cc. Menene ya ba mutum wannan damar? Cikin suratul Sajda Allah ya ce
Q32:9 “Sannan ya daidaita shi, kuma ya hura a cikinsa da ga ruhinsa, kuma ya sanya muku ji da gani da zukata (Na fahimta). Godiyarku kadan ce kwarai”   
Dukkan halittu babu wanda ya sami wannan kyauta ta Ubangiji. Amma mutum ya kasance da zuciya, wato kwakwalwa wadda ta habaka fiye da sauran sassa na jikinsa kuma Allah ya hore mata fahimta (Intelligence) fiye da sauran dabbobi, amma kwayoyin halitta iri guda (cells) ne su ka yi kwakwalwar mutum da ta dabba. Tsarin kwakwalwa ta mutum da ta dabbobi a bangaren sashen da ya ke kula da fahimta (intelligence), tunawa (memory) da magana (speech) su ne su ka sha banban da ta dabbobi. A cikin suratul Rahman Allah ya ce mana:
Q55:3-4 “Ya halitta mutum, ya sanar da shi magana”
Sashen da ke kula da magana, a kwakwalwar mutum ne kawai ya inganta har ya bashi damar samar da yare na magana domin wasu su fahimce shi. Dabbobi na da hanyoyin sadarwa a tsakaninsu, amma na su na wani dan takadirin manufa ne. Misali su na da kuka iri-iri wanda kowanne kuka na da ma’anarsa, ko dai kira domin barbara, ko sanar da ‘ya’ya wani hadari, kare kai ko muhalli, nu na hanya ko jin yunwa d.s.s. Haka kuma su na da alamomi da ke nu na tausayi,tsoro, kauna d.s.s. Cikin suratul Balad Allah ya ce:
Q90:8-9 “Shin ba mu sanya masa idanu biyu ba? Da harshe da lebba biyu?”    
Wato ta hanyar amfani da abinda ido kan gani da Kuma baki, wa to lebba, harshe, makogwaro da iskar huhu wani kan iya sanar da wani don a fahimce shi ta amfani da kalmomi ko a rubuce. Wannan tsari mutum ne kadai Allah ya hore ma cikin halittun duniya, wanda shi ne babban ginshikin da ya banbanta shi da sauran dabbobi. Ta hanyar magana da yare mutum ya sami damar fahimtar ilimi, tara shi da yada shi wanda ya kuma bashi damar mamaye duniya. Ta hanyar rubutu, Dan Adam ya kasance yana iya mika al’ada daga kakanni, zuwa iyaye da jikoki. Hakan ya bada damar alkinta tsarin rayuwar al’umma gaba daya (civilization) kama daga fasaha, tattalin arziki, shari’a, ilimi da sauransu tsawon dubban shekaru. Ta hanyar iya magana shi ne ya ba mutum damar sadarwa da Ubangijinsa kamar yadda ayar taci gaba da cewa:
Q90:10 “Kuma ba mu shiryar da shi ga hanyoyi biyu ba?”
Shi kansa yare asalinsa kamar komai ya fara ne da ga yare guda. Kamar yadda
Allah ya ce mana cikin suratul Baqara
Q2:213 “Mutane sun kasance al’umma guda”
Al’ummar farko a doron kasa sun kasance guda, yare guda, al’ada guda babu banbance-banbancen jinsuna. Abubuwan da su ka haifar da samuwar sabbin yaruka sun hadar da kaura da ga wani sashe zuwa wani, banbancin yanayi da karuwar mutane ya haifar da sabbin kalmomi da hanyoyin fadarsu. Ta haka sabbin yaruka su ka fara samuwa. Yare wani abu ne tamkar mai rai domin dai ana haihuwarsa (Wato fara amfani dashi) ya na girma, ya tsufa da ga bisani kuma ya kan mutu. Misali akwai yaren Latin, wanda a shekarun baya babu wani yare na yada ilimi kamar sa (tamkar yadda turanci yake a yanzu) amma sai gashi a yanzu babu wa ta al’umma da ke amfani dashi. Haka kuma akwai yaren Hibrisanci, yaren mutanen Annabi Isa, wanda shekaru 2000 da su ka wuce ya na kan ganiyarsa amma yanzu ya tsufa domin sai dai a littattafai kawai ake amfani dashi.
A takaice, mutum ya kasance daga wata halitta wadda ta fara Rayuwa a doron kasa kasa kamar ta sauran dabbobi, a yau mun kasance masu saka kayayyaki a jiki na alfarma sabanin yawo tsirara ko da ganye. Mun kasance masu zama cikin gidaje na gilashi da zinare, sabanin zama kan dutse ko cikin kogon dutse. Mun kasance masu iya ratsa tekuna ta samansu da karkashinsu, haka kuma muna keta sararin subhana da ma tura jirage masu sarrafa kansu. Mun gama mallake wannan duniya tamu ta kowacce fuska. Duk wadannan abubuwa sun faru ne sakamakon tsarin halittar kwakwalwa mai fifiko wadda Allah ya yi mana. Nan gaba, Allah kadai ya san abinda jikokinmu zasu iya yi domin duk wannan ci gaba da muke da shi a yanzu ya samu ne sakamakon a yanzu muna iya amfanar kasa da kashi 10% ne kacal na abinda kwakwalwarmu ke iya yi. Me kake tsammani nan da shekaru masu zuwa idan aka ce jikokinmu zasu iya amfanar ko da kashi 50% ne na iya karfin kwakwalwarsu?
 

Comments

Popular posts from this blog

BAKAR TAURARUWA (BLACK HOLES)

RUKUNIN TAURARONMU-RANA

TSUNTSAYE