HADARIN CANJIN YANAYI
Duniyarmu
idan ka kalle ta a dunkule yadda take, tamkar halitta guda ce domin Allah ya
tsara ta yadda ta ke da tsarin daidaita kanta da kanta, yadda za ta ci gaba da
kasancewa mattattara ta halittu masu rai da marasa rai. Wannan tsari na
daidaiton duniya ya kan sami nakasau idan wani abu ya yi yawa fiye da yadda ya
kamata wanda a sakamakon haka sai ya yi illa ko kawo canji ga sauran tsarin.
Tun sanda aka samar da duniya sama da shekaru biliyan hudu da rabi da su ka
gabata, tamkar jariri da aka Haifa, haka duniya ta rika habaka sannu a hankali
wato daga wani dunkule na wuta har ta huce ta zama kasa sannan ruwa ya samu
wanda daga cikinsa kuma Allah ya samar da halittu masu rai. Tun sanda rayuwa ta
fara a doron kasa, an sami halittu iri-iri wadanda su ka iya zama su rayu a
sassan duniya daban-daban, kama daga doron kasa, karkashin ruwa da cikin iska
da ke sararin duniya har ma da can karkashin kasa inda ya ke da tsananin zafi.
A
dogon tarihin duniya an sami canjin yanayi daga zafi mai yawa zuwa ga sanyi mai
tsanani, wanda ke samuwa sakamakon abubuwa da dama. Cikin manyan abubuwan da ke
kawo canjin yanayi a duniya shine yanayin sanyi ko zafi wanda shi kuma ke
samuwa sakamon yadda duniya ke juyawa da zagaya rana, sannan akwai yanayi yadda
farantai da ke dauke da nahiyoyin duniya ke motsawa, da kuma shi kansa
maganadisun duniya da ke da karfi a dorayen duniya na kudu da arewa. Wadannan
abubuwa kan sa dumin duniya ya karu ko ya yi kasa, yayin da ya yi kasa sosai shine
ake samun yanayin hunturu mai tsanani a duniya sakamakon kankara da ke mamaye
yawancin sassa na duniya. Ko a lokacin ruwan dufana a zamanin Annabi Nuhu irin
abinda ya faru kenan sakamakon ruwa ya mamaye duniya sai duminta ya yi kasa
sosai yadda wurare da dama su ka daskare su ka zama kankara. A tsawon tarihin
duniya an sami yanayi irin wannan sau biyar tun kafin ma zuwan Dan Adam. Wannan
canzawar yanayi daga zafi zuwa sanyi, duniya da kanta ke kula da tsarin wajen
daidaita shi.
Yanayin
sanyi da zai zo nan gaba sabanin wanda aka saba gani ne a baya, saboda zai samu
ne sakamakon yadda Dan Adam ke amfani da wannan gida da Allah ya bashi, ta
hanyar dumamar yanayi wanda ayyukanmu ke haifar da shi. Allah ya tsara duniya
yadda akwai wata rumfa da ke kare mu daga zaruruwan hasken rana masu illa
wadanda ba domin wannan rumfa ba, rayuwa a doron kasa za ta yi wahala. Wannan
rumfa, da iska Allah ya samar mana da ita sakamakon kwayar zarra ta halittar
iskar oxygen da ke sararin sama wadda idan zaruruwan hasken rana masu illa su
ka doke ta sai ta canza, sakamakon dahuwa, ta koma wata samfurin iskar wadda
ake kira ozone. Ita ozone maimakon zaruruwan haske su dafa ta kamar oxygen, sai
ta zama kamar wani bango na madubi wanda idan sun dake ta sai su yi tsalle baya
su koma sama’u maimakon ratso rumfar su iso doron duniya. Wannan iska ta ozone
ta yi cincirindo a kimanin kilomita 20-25 idan ka yi can sama, kuma fadinta ya
kai kimanin kilomita 60. Don haka wannan rumfa ta ozone ita ke kare halittu
daga gurbatattun abubuwa masu guba da za su iya hallaka halittu a doron kasa.
Sakamakon kulafucin dan Adam na tarawa da more abin duniya ta hanyar
masana’antu da kone-konen dazuka da sauran hanyoyi na gurbata muhalli, shi ke
samar da kwayar iskar Co2 wadda idan ta tashi sama ta cakudu da kwayar iskar
ozone sai ta sake maida ta kwayar oxygen wadda bata iya bada waccan kariya. A
yanzu haka an gano cewa hujewar wannan rumfa a sashen doron duniya na arewa,
sakamakon irin wadancan ayyuka, ya kai fadin murabba’in kilomita miliyan 20.7
(wato misalin fadin kasar Nigeria sau ashirin da daya kenan). Sannan akwai wasu
sassan da su ka huje bayan wannan a wasu sassan na duniya.
Wannan
hujewa ta samo asali tun daga lokacin da Dan Adam ya gano kirkirar masana’antu
kusan shekaru 300 da su ka gabata a turai, kuma a tsawon wannan lokaci dumamar
duniya ya karu da kimanin digiri 3 a ma’aunin zafi kuma ya na karuwa sannu a
hankali. Wata babbar illar kuma ita ce ta sare dazuka a fadin duniya domin
samar da itace ko katako da filayen noma ko aikin tituna da gidaje. Ana kiyasin
cewa a duk minta daya ana sare itatuwa daidai da fadin filin kwallon ball a
kowanne minti guda a fadin duniya, kuma ba tare da sake dasa wasu itatuwan ba.
Wutar daji, wadda yawanci manoma ke haifarwa wajen share filayen gonaki na daya
daga cikin abinda ke haifar da karuwar hujewar wannan rumfa da ta zamar mana
garkuwa.
A
yanzu mun fara ganin illar abubuwan sakamakon wayar gari yananyi na ta canzawa
da haifar da fari a kasashen afirka, ambaliyar ruwa a kowanne sashe na duniya,
wutar daji musamman wadda ba’a taba ganin irinta ba a bana a can kasar
Australiya wadda ta lakume halittu kusan biliyan daya da miliyoyin filayen
daji. Sannan mu na gani yadda kankara ke ta narkewa a doron duniya na Arewa
(Arctic) da na kudu (Antarctica). Kuma narkewar wannan kankara na kara yawan
ruwa a tekunan duniya yadda ambaliya ta ke ta karuwa musamman a garuruwan da ke
gabar teku. A nan gaba idan wannan narkewa ta kankara ta ci gaba a yadda take
faruwa yanzu saboda dumamar yanayi, garuruwa da ke bakin gabar teku irinsu
Lagos nan da yan shekaru kadan ruwa zai mamaye su. Ruwan sha da ake samu daga
rafuka da koramu sai ja baya ya ke yi yadda ya fara zama gwal a sassa da dama
na duniya kuma masana su na hasashen cewa nan da yan shekaru masu zuwa yadda
ake yake-yake a yanzu a kan man fetur haka za’a koma yakoki a kan ruwan sha.
Kuma mun ga yadda a yanzu ake tada jijiyar wuya tsakanin kasahe irinsu Egypt da
Ethiopia game da ikon tare ruwan kogin Nilu da Kasahen Turkiya, Syria da Irak
akan koguna Eupharates da Tigris, Afghanistan da Iran kan Kogin Helmand,
Turkiya da Armenia, a kasashen Yemen, China, India, Somalia da Bolivia har mu
nan a Nigeriya an fara kai ruwa rana da Nijar kan kogin Kwara.
Halayyar
dan Adam ta hadama wajen kwakulo ma’adinai daga karkashin kasa irinsu man
fetur, kwal, sumunti, kuza da sauransu hakika ya shake wannan duniya tamu tare
da wargaza tsarinta na daidaito, abinda idan ba mu gyara ba shi zai jawo
hallakarmu gaba daya. Hakika ba zamu iya kaucewa bukatunmu na yau da kullum ba,
gami da hayayyafarmu amma dai za mu iya canza yadda mu ke biyan wadannan bukatu
ta hanyar bin hanyoyi da zai ci gaba da baiwa duniya damar ci gaba da tsarinta
na daidaito. Za mu iya yin haka ta hanyoyin yin amfani da hasken rana da iska
da ruwa wajen samar da hasken lantarkin da mu ke bukata da kuma makamashi na
masana’antu da ababen hawanmu.
Babbar
matsalar canjin yanayi shine kasashe matalauta irinsu Nigeriya su ne za su fi
dandanawa wajen jin radadin, maimakon manyan kasashe irinsu Amurka da Turai da
Chana wadanda su ne ja-gaba wajen kawo gurbacewar yanayi. Wajibi gwamnatoci da
mutane su tashi tsaye domin ganin mun canza yadda muke abubuwa a kokarin rage
dumamar yanayi da ke ta’azzara canjin yanayi. A Najeriya wajibi ne mu fara
tunanin yadda za mu yi wajen tarar wannan annoba da wuri, kafin ta cimmana.
Hanya mafi sauki shine mu fara saka kudade wajen samar da lantarki da makamashi
ta hanyar hasken rana wanda Allah ya bamu da kuma iska. Sannan dole jihohin
arewa su hadu waje guda wajen ganin sun gina bangon-bishiyoyi wanda tun 1999
karkashin Obasanjo aka fara maganar har aka kafa kwamiti karkashin Atiku
Abubuakar domin aiwatar da aikin amma zancen ya bi ruwa. Idan aka gina bangon
bishiyoyi daga Maiduguri zuwa Sokkwato hakika kwararar Hamada za ta tsaya cik.
Sarakunan mu dole su shigo cikin wannan lamari kamar yadda sarakanmu a baya su
ka zama jagorori wajen dashen bishiyoyi. Kwararar Hamada an kiyasta yana
kwaranyar tsawon kilomita guda duk shekara, wanda idan ba’a yake shi ba wallahi
za’a wayi gari Hamada ta kai teku. A sakawa yaran makaranta cikin sharuddan
karbar shaidar kammala karatunsu su dasa bishiya kamar yadda wata kasar
gabashin Afirka ta saka. A zamanin tsohon gwamnan Kano Audu Bako ya kirkiri yin
irin wannan bango na bishiyoyi a yankin Kazaure da Danbatta abinda ya taimaki
yankin wajen yakar Hamada kuma yanzu idan ka shiga wajen zaka tarar ya zama
daji. Da a ce tun wancan lokaci sauran sassan arewa sun kwaikwayi Audu Bako da
yanzu an samar da wannan kariya ga arewacin kasar nan. Wajibi mu farfado da
wannan tsari.
Maganin dumamar
duniya da samuwar canjin yanayi sune canza yadda muke rayuwa tare da juya
akalarmu zuwa ga makamashi mai tsafta wanda za’a iya jujjuya shi: irinsu rana,
iska da ruwa. Sannan dole a yaki sare bishiyoyi ta hanyar dasa sabbi. Kasashen
Turai sun ware asusu na Euro miliyan dari domin taimakawa kasashe irin su
Nijeriya wajen yaki da canjin yanayi, don haka wajibi daidaikunmu da
gwamnatocinmu mu tashi tsaye wajen ganin cewa ko da gangamin dashen bishiyoyi
mun fito da shi wanda zai bamu damar samun wadancan kudaden tallafi domin yakar
annobar da ke gabanmu. Idan yanayin sanyi gama duniya (Ice Age) ya dawo da
wuri, yadda wasu masana ke hasashe, mu sani cewa turawa da kasashen da su ka ci
gaba za su iya jurewa su rayu, amma wallahi mu macewa zamu yi gaba dayanmu
saboda ba mu da karfin tattalin arziki ko tsari da za mu iya tunkararsa. Idan
kunne ya ji….
Comments
Post a Comment