JUJJUYAWAR ISKOKI


Iska kamar ruwa da wuta ginshiki ce ta rayuwar dukkan halittu walau dabba ko tsirrai. Masana sun rybuta dubban littattafai akan yanayin iskoki, kuma a kullum suna kara fahimtar ta da irin amfanoninta. Allah kansa yayi mana bayanai iri-iri cikin Qur’ani a game da iska. Misali cikin suratul Jasiya
Q45:5 “Da jujjuyawar iskoki, akwai ayoyi ga mutane masu hankali”
Juyawar iskoki a doron duniya al’amari ne da dole ya burge duk wani mahaluki da ke amfani da kwakwalwarsa don yin tunani, domin akwai tsari da ka’idoji da suke bi. Juyawrsu ta ta’allaka ne akan yanayin zafi ko dumi (temperature) na sashe ko nahiyoyi. Shi yanayin zafi/dumi na samuwa ne kai tsaye daga zafin rana. A yayin da zaruruwan zafi (heatwaves) da ke sauka daga rana, su kan dafa wani sashe na iska. Nan da nan sai ita dafaffiyar iska ta doshi inda yake da sanyi, wato idan ta sama ce sai ta doshi kasa idan kuma ta kasa ce sai ta doshi sama, haka nan idan ta gaba ce sai ta doshi baya idan kuma ta baya ce sai ta doshi gaba. A lokacin zafi iskokin da ke juyawa a saman nahoyoyi suna da dumi sosai don haka sai su rika kadawa wajen teku, domin a lokacin tekuna sun fi nahiyoyi sanyi. Amma a lokacin sanyi kuma iskoki da ke saman nahiyoyi su na da sanyi don haka iskokin da ke saman nahiyoyi sun fi su dumi, sai iska ta rika kadawa daga bangaren teku zuwa tudu. Kasancewar duniya kamar kwallo ta ke, akwai layin da ya raba ta gida biyu daga kudu zuwa arewa (shi ake kira da equator). A sashen arewacin duniya, doron duniya na arewa (Arctic) ya na lullube da kankara don haka waje ne mai sanyi shi yasa sai iska dake wannan sashe ta rika kadowa daga can ta doso wannan layi da ya raba duniya. A yayin da iskar ta zo gab da da wannan layi, sakamakon juyawar da kwallon duniyar yake yi a matsanancin gudun da ya kai Km 1000 a cikin awa daya, sai hucin wannan juyawa ta karkatar da iskar da ta doso tsakiyar daga arewacin duniya ta karkata ta yi sashen arewa-maso-gabas. Don haka a kowane lokaci juyawar iska a sashen arewacin duniya (Northern hemisphere) haka ya ke kasancewa.
A sashen kudancin duniya kuma, doron duniya dake kudu (Antarctica) shima kankara ce don haka iska na kadowa daga can ta doso tsakiyar duniya (Equator) amma yayin da ta zo dab da wurin sakamakon hucin juyawar duniya sai ya karkatar da iskar ta doshi sashen Kudu-maso-gabas. A kudancin duniya (Northern Hemisphere) shima haka nan kowanne lokaci iska ke jujjuyawa.  A takaice iska a arewacin duniya na zagayawa tamkar ka saka hannun agogo ya bi ta baya (Anti Clockwise), kuma a sashen kudancin tana zagaye kamar yadda hannun agogo ke bi (Clockwise). Su kansu doron duniya guda biyu da ke koro iska, doron arewa na kada iska sashen gabas shi kuma doron kudu na kada iska sashen yamma.
Yanayin dare da rana shima ya samar da yanayin da iska ke bugawa, misali da rana iska na kadowa daga teku saboda a lokacin tudu ya fi teku zafi, dalili kuwa shine shi teku na daukan lokaci kafin ya dumama amma tudu da wuri ya ke daukan zafi. Don haka da rana sai iska ta rika kadowa daga teku, amma da dare kasancewa tudu ya fi teku saurin hucewa sai iskar ta rika kadawa daga tudu zuwa teku.  A sassan tsaunuka kuma iska kan gangaro daga saman tsauni zuwa kasa. Cikin suratul Zariyat sai Allah ya ce
Q51:1 “Ina rantsuwa da iskoki masu watsa abubuwa, watsawa” 
Tun lokacin da Allah ya halicci iska ya bata aiki da tsare-tsarenta. A nan duniya ma iya cewa babu wani abu da ke da mahimmanci wajen watsa abubuwa ko mu ce sadarwa. Sannu a hankali Dan Adam yana ta gano hanyoyi na amfani da iska, misali idan ka dauki sauti iska ce ke da alhakin watsa shi daga wan bangare zuwa wani a cikin iska ko ruwa ko dunkule. Idan da za’a zuke iska gaba daya a yau da duk wata halitta ta daina jin sauti. Haka nan iska ce ke dauke da zangon rediyo (Radio waves), shi zangon rediyo shine ke kunshe da zaruruwan zangon Talabijin, Tangaraho, Rada, Na’ura mai kwakwalwa da sauransu. Sakamakon gano wadannan zaruruwa, ya baiwa Dan Adam damar sadarwa ta hanyar sauti, hoto da rubutu (Radio, Tv, Computer d.s.s) daga kowane bangare na duniya kai tsaye. Zaruruwan zangon rediyo suna da tsananin gudu domin suna tafiya ne kamar ta haske wato a gudun da ya kai Km 186,00 a sakan daya. Wannan shi yasa da ake samun damar da an watsa wani abu cikin wadannan zangogi nan take suke isa inda ake karbar su (Live broadcast). Annabi Muhammad (SAW) a cikin wani hadisi nasa ya ce duniya ba za ta tashi ba har sai wanda yake a karshen duniya a bangaren gabas yayi magana da wanda yake bangaren yamma.
Har ila yau iska ita ce ke rarraba zafin rana zuwa sassa daban-daban, wanda hakan ke da tasiri sosai wajen yanayi. Bangarorin duniya da ke da kurmi (Tropical) sun fi sauran sassa samun dumi domin dumin da suke samu yafi wanda suke rasawa. Amma bangarorin da ke da sanyi ko kankara suna da karancin dumi domin dumin da suke rasawa yafi wanda suke samu. Iska ita ce ke daidaita dumin da duniya ke samu da wanda take rasawa a tsawon shekara. Allah ya ci gaba da cewa
Q51:2 “Sannan da iskoki masu daukar nauyi”
Nauyin da iska ke kwasa a kullum ba zai iya misaltuwa ba, domin idan ka dubi irin yawan ruwan da iska ke kwasa a matsayin turiri daga numfarfashin halittu, tsirrai, koramu da tekuna ya isa. Masana yanayin sararin samaniya sun kiyasta cewa turirin da iska ke kwasa zuwa sama, wanda ke yawo a matsayin hadari ko gajimare, idan da a lokaci guda zasu narke su zubo a matsayin ruwan sama to da lallai duniya gaba dayanta ta zama a karkashin ruwa don ko ina sai ya zama lullube da ruwa.  A takaice tekuna ne ke yawo a sararin sama. Allah ya ce
Q15:22 “Mu ke aika iska mai Barbara”
Kamar yadda na fada a baya iska ce ke rarraba abubuwa, mun ga bayani yadda ta ke rarraba sauti, zafin rana da turirin ruwa. Wani gagarumin aikin da iska ke yi shine na rarraba iri na tsirrai, wato fiye da rabin tsirrai sun dogara ne a kan iska wajen Barbara saboda iska ce ke kwasar kwayoyin manniyyi na bishiya zuwa ga macen bishiya. Kusan duk tsirran da muka fi amfani da su irinsu shinkafa, alkama, dabino, gwanda da sauransu wannan tsari suke bi wajen samar da fure da ‘ya’yansu. Cikin suratul muminun Allah ya ce
Q23:18” Muka saukar da ruwa daga sama daidai gwargwado sannan muka zaunar da shi a cikin kasa, alhali kuwa lallai ne mu , a kan tafiyar dashi masu iyaw ne”
Sanin kowa ne cewa ruwa shine ginshikin samuwa da wanzuwar halitta, to shi kansa ruwan iska ce ginshikin samar da shi da kuma rarraba shi. Ruwan sama ya fara samuwa ne a doron duniya biliyoyin shekaru da suka shude ta hanyar zafin rana mai tsanani da ke sauka kai tsaye doron duniya, wadda ke cike da aman wutar duwatsu. Wannan aman wuta yana fitar da samfurorin iskoki daban-daban wadanda zafin ya ke dafa su har suka zama turiri wanda daga bisani ya zama hadari. Kwayar ruwa kanta wasu samfurorin iska ne guda biyu wato Oxygen da Hydrogen idan suka dunkule waje guda suke samar da digon ruwa. Wannan hadari na farko shine ya narke yayi ta zubar da ruwa tsawon shekaru kusan 60,000 inda ya cika koguna da tekuna. Tun daga farkon duniya kawo yanzu wannan tsari Allah ke amfani dashi wajen samar da ruwan sama, wato a duk lokacin da zafi ya karu sosai (temperature) sai kwayoyin ruwa su canza su zama turiri wanda iska ke kwasa zuwa sama. Yayin da ake yin sama da wannan turiri sai ya rika hucewa har ya kai matsayin ya fara daskarewa ya zama hadari. Hadari kansa iri uku ne
-Hadarin kasa-kasa: Wanda ke daskarewa a wajen kilomita 1.5 daga doron duniya, irin wannan hadari za’a ganshi fatsi-fatsi mai duhu kuma yakan lullube sararin sama, a cikinsa digo-digon ruwa ne.
-Hadarin tsakiya: Wanda ke daskarewa a wajen kilomita 6 daga doron duniya. Yana da kauri da launin shudi-shudi, shima yana dauke da digo-digon ruwa. A irin wannan hadari ne ake samun bakan-gizo, shi bakan gizo sabanin fahimtar malam bahaushe ba wai yana shanye ruwa ba ne a’a, hasken rana ne ke ratsowa daga bayan hadarin ya rarrabe launuka da ke kunshe cikin hasken rana. Misali idan ka sami dalar gilashi (prism) ka kara a saitin hasken rana da zarar hasken ya ratsa ta cikinta sai ta rarrabe hasken rana zuwa launukan nan guda bakwai irin na bakan gizo
-Hadarin can sama: Shi kuma yana daskarew ne daga turiri a wuraren kilomita 8 daga doron duniya, shi fari-fari ne kuma sirara ne. Wannan hadari akasarinsa kunshe yake da kankara.
Yayin da ire-iren wadanan hadari suka narke shi ke samar da ruwan sama, kankara, dusar kanakara ko yayyafi. Shi kansa yanayin zubar ruwan sama, kankara ko yayyafi yana samuw ne sakamakon aikin iska domin ita ce ke rarraba shi zuwa digo-digo ko dunkule (ba don aikin iska ba yaya zaka ga cewa ruwa na zuba bagatatan? ai da tabbas illarsa sai ta fi alherinsa yawa).
Bangarorin duniya da ke da danshi sosai (kamar kurmi) sun wuraren da suke fako (kamar sahara) saboda danshin da ke tashi sama shi ke samar da yawan ruwa da ke zuba a waje. Ciki hadari a ke samun walkiya da tsawa, walkiya na samuwa ne sakamakon kasancewr hadarin na da cajin lantarkin nan guda biyu wato + da – (mai karbar wuta da mai bayar wa). Allah ya tsara hadari yadda daga samansa akwai kwayoyin lantarki masu bada wuta sannan daga kasan sa akwai kwayoyin lantarkin masu karbar wuta. A duk lokacin da suka gwamutsu, nan take sai su samar da haske na walkiya tamkar ka jona wayoyin lantarki guda biyu ai zaka ga sun yi toci. Sakamakon walkiyar sai ta saka hadarin ya dumama cikin gaggawa wanda ke tarwatsa kwayoyin iska da ke ciki har su fashe. Wannan fashewa ita ke haifar da tsawa mai rugunniya. Wannan ne dalilin da ya sa sai ka ga walkiya kafin ka ji tsawa.
 
 

Comments

Popular posts from this blog

HUJJOJIN TASHIN KIYAMA A KIMIYANCE

WUTA

RUWAN DUFANA