KETA SARARIN SUBHANA
Tsawon
miliyoyin shekaru babban abinda ya fi jan hankali da burge Dan Adam shine yadda
Tsuntsaye da kwari ke iya tashi sama. Wannan burgewa ta zama kishi domin
mutane, duk da cewa Allah bai hore musu wata halitta a jikinsu da za su iya
tashi ba, amma an yi ta kokarin kirkirar fuka-fukai don kwaikwayon halittu masu
tashi. Mutane daban-daban daga al'ummomi da dama sun gwada tashi sama ta hanyar
kwaikwayo, wanda ya haifar da asarar rayuka da kuma rasa gabobi. Duk da cikas
da aka fuskanta maimaikon kokarin ya ragu sai ya ringa habaka. Cikin suratul
Rahman sai Allah ya ce mana
Q55:33"
Ya ku (gungun) aljanu da mutane, idan zaku iya ketasararin sammai da kasa, to
ku keta. Amma sai da izinin Allah zaku iya ketawa"
Wannan
aya ta zama daya daga cikin ayoyin mu'ujizar Qur'ani domin ta fadi wani abu da
zai faru a gaba.
Abbas
Ibn Firnas, mutumin Kasar Andalusia wanda ya rayu a garin Cordoba, shine
masanin kimiyya na farko a tarihi wanda ya fara kera jirgin sama mai fuka-fuki
kuma ya tashi sama ya yi zagaye har na kimanin mintuna goma a gaban bainar
jama’a a shekarar 875 AD, wato kusan karni biyu da rabi bayan wafatin manzon
Allah. Amma kamar yadda turawa su ka saba sace wa musulmi darajar farko ta
kirkirar abubuwa da dama, ya sa ba’a jin sunan wannan dan taliki a hurumin
mutum na farko da ya fara kera jirgin sama. Wannan bincike na sa bai sami ci
gaba ba har daular musulunci ta Andalus ta rushe, amma ina zaton aikinsa ne ya
janyo mashahurin masanin kimiyya na kasar Rum, wato Leonardo Da Vinci (1452),
bayan kimanin shekaru 600, ya ba shi karsashin nazari a wannan fage inda har ya
yi wasu zane-zane da ke nuna za'a iya kirkirar na'ura da za ta iya tashi ba
tare da an kwaikwayi yin fuffuke irin na dabbobi ba. Duk da haka wannan zane
bai yi tasiri ba har bayan kimanin shekaru 400 da mutuwar sa. A farkon karnin
da ya gabata ne cikin shekarar 1903 wasu yan uwa guda biyu (Wilbur Brothers) na
kasar Amurka su ka cimma nasarar yin inji na farko da ya bar doron kasa kuma
yayi tafiya a cikin sararin samaniya. Wannan nasara ta samu ne sakamakon gane
amfani da hanyoyin nan guda hudu dake ba kowane abu mai tashi damar iyo a cikin
iska (4 forces of Aerodynamics) wato Ingiza (Thrust), Tirjiya (Drag), nauyi
(Weight) da kuma karfin dagawa sama (Lift). Samun daidaiton wadanna abubuwa ke
bada damar iyo a iska domin ingiza na samuwa ne daga karfin na'ura da kuma
iska, haka nan tirjiya na samuwa ita ma daga na'ura da iska sai kuma karfin
dagawa wadda ta ta'allaka ga nauyi dake dogaro ga maganadisun dake jan komai
kasa (Gravity) wadda karfin inji ke iya gujewa. Ko daga wadannan abubuwa da ke
baiwa jirgi ikon tashi sama, mai lura na iya gane cewa babu wani abu da zai iya
tashi sama sai da izinin Allah domin da zarar Allah ya zuke iskarsa kuma ya
dankare maganadisu (Gravity) to babu wani abu da zai iya dagawa sama ko da kuwa
bai kai auduga nauyi ba.
Bayan
wadancan abubuwa hudu da dole sai sun hadu ake iya tashi sama, akwai kuma wasu
abubuwa dake da tasirin gaske wajen sauka da tashin jiragen sama:
--Yanayin
Dumi (Temperature): da ke haifar da yadda iska zata kasance wajen nauyinta
(Density) na daya daga ciki. Idan iska bata da nauyi jirgi ba zai iya tashi ba
amma idan tayi nauyi sai ya iya tashi
--Iska:
har ila yau, iska da ke kadawa ita ce ke bada saitin bangaren da jirgi zai
tashi ko kuma ya sauka domin baya tashi sai ta daura da nahiyar da take kadawa
haka wajen sauka sai ta daura da nahiyar da iskar ke kadawa (wato idan iska na
kadawa yamma sai jirgi ya sauka ta gabas), shi yasa ake ganin wani jan kyalle
mai kama da bututu a gefen titin da jiragen sama ke tashi, ya na nuna inda iska
ke kadawa
--Layukan
tsaye da na kwance a doron duniya (Longitudes da lattitude): na taimakawa
matuka jirgi wajen gane nahiyoyi
--Mahadar
wadancan layuka (Co-ordinates): Dukkan garuruwan dake doron kasa na da mahadar
wadannan layuka da ke kusa da su kuma na kano daban yake da na kaduna ko Abuja.
Shine yasa duk da cewa babu tituna a sama kuma matukan jirgin sama ba sa iya hangen
doron kasa amma amfani da wannan mahada ya na sa su gane sun zo inda za su je
ba tare da hakikanin ganin wajen ba
--Doron
maganadisun duniya na arewa (North magnetic pole): Wanda duk ya san compass da
ake sawa a dardumar sallah don nuna al-qibla yana ganin wata allura da ke
kwance ta na nuna nahiya. To ita allurar a koda yaushe ta na fuskantar inda
wannan maganadisu na arewa yake don haka a duk inda ka ke da zarar ka gane
arewa dole ne ka gane ina sauran jihohin gabas, kudu da yamma su ke.
--Zangon
rediyo (frequency) Tukin jirgi ba zai yiwu ba sai da zangon rediyo domin kusan
mafi mahimmancin na'urorin da ake amfani da su ta hanyar zangon rediyo ake
amfanin da su, misalin na'urarorin da ke amfani da zangon rediyo wajen
jagorancin jirgi a wajen sauka (ELS), da na'urar gane nisa (DME), da na'urar
gane nahiya nan take (Automatic direction finder) da kuma naurar tangaraho da
rada dukkanninsu ta zangon rediyo ake amfani dasu.
Wadannan
abubuwan da na lissafa sai da su jirgin sama zai iya tashi kuma dukkansu babu
wani abu da bai dogara da wani abu halittacce daga ubangiji ba. Hatta shi kansa
injin jirgi da mutum ne ya kirkire shi ba zai yi aiki ba sai da iska da Allah
ya halitta. Domin ga yadda injin jirgi ke aiki: wato da zarar an kunna shi sai
wasu manyan farfeloli da ke ciki su fara juyawa a guje kuma an kera su yadda
idan suna juyawa sai su dinga zukar iska daga waje da karfin gaske (da mutum
zai tsaya saitin su sai iskar ta fizgo shi cikin injin). Da zarar iskar ta
shiga cikin injin sai ta dunkule saboda karfinta da kuma rashin sarari, sai a
watsa mata fetur wanda zai sa ta fara konewa cikin gaggawa (idan ka leka cikin
injin sai kaga wuta ce ta ke ci gagga-gagga) wannan konewa sai ta dada
kumburawa da fadada wannan iskar yadda dole sararin wajen zai mata kunci dole
ta nemi hanyar ficewa cikin gaggawa. Fitar wannan iska da karfi ke baiwa jirgin
kuzarin zabura (misali shine idan ka cika balan-balan kuma sai ka saki bakinta
za ka ga ta fice a guje tana zarya). A takaice haka ne yadda injin jirgi ke
aiki, ka ga lallai shi kansa idan babu iskar da Allah ya halitta ba zai yi
tasiri ba. Wannan shine manufar waccan aya da Allah ke cewa sai fa da izininsa
za a iya keta sararin sama.
A yau Dan Adam ya kai
tsaikon ba jiragen sama wadanda ke kara-kaina a doron duniya ba, har wadanda ba
su da matuka an kirkira su na tafiye-tafiye zuwa wasu duniyoyi da ke cikin
rukunin tauraron mu, wato Rana. Cikin irin wadannan jirage wanda ya fi shahara
sune yan tagwayen jiragen da kasar Amurka ta harba daf da juna a shekarar 1977
wandanda aka yi wa lakabi da Voyager I da Voyager II. A yanzu haka shi wannan
jirgi na Voyager 1 da ke gudun kilomita dubu 61,200 a awa guda, a ranar yau ta
20 ga watan Mayu na 2019, ya yi tafiyar shekaru 41 da wata 8 da kwana 15, tun a
shekarara 2012 ya fice daga rukunin tauraronmu. Ya kasance jirgi na farko da ya
iya dauko hoton jerin rukunin duniyoyi da ke kewaya rana. Wannan jirgi zai ci
gaba da lulukawa sama’u har zuwa shekarar 2025 lokacin da na’urorinsa za su
daina aiki. Tsarki ya tabbata ga ubangiji wanda ya baiwa Dan Adam irin wannan
basira ta kera jirgi wanda ake sarrafawa daga doron duniya, ya yi tsawon
shekaru ya na tafiya tare da bada bayanai na hotuna ga abubuwan da ya ke karo
da su. A wannan jirgi ne Carl Sagan ya sa aka dauki sautin gaisuwa da yaruka
daban daban na duniya ko da Allah ya sa watarana wannan jirgi zai karo da wasu
halittu a hanyarsa.
Comments
Post a Comment