KUDAN ZUMA
Kwari su ne jinsin dabbobi da suka fi kowacce dabba yawa a
wannan duniya tamu. Ana samun su a kusan kowacce nahiya, kuma ayyukansu don
amfanin rayuwar Dan Adam ba zai misaltu ba. Su ma ba’a bar su a baya ba cikin
irin halittun da Allah yayi mana bayanin su cikin Qur’ani. Allah ya kawo mana
maganganu a kan kuda, kudan zuma, tururuwa, gizo-gizo da sauransu. Dukkan
abinda Allah ya ambata cikin Qur’ani zaka idan kayi bincike tarar daa shi da
cikakken tsari na kimiyya wanda kafin zuwan Qur’ani babu wani cikakken bayani
na kimiyya a kansa. Bari mu duba kudan zuma, saboda babu wani kwaro da masana
kimiyya suka yi bincike a kansa kamar shi. Cikin suratul Nahli Allah yace
Q16:68 “Kuma ubangijinka yayi wahayi zuwa ga kudan zuma cewa “ka
riki gidaje daga duwatsu, kuma daga itace, kuma daga abinda suke ginawa”
Wannan aya ta fara da tabbatar mana da cewa dabbobi ma ana yi
musu wahayi, domin ba don wannan wahayi ba ta ina zasu rika tafiyar da
rayuwarsu a tsare kuma cike da ilimi? Shi wannan wahayi kai tsaye Allah ke yi
musu shi ba tare da wani manzo ba. Kowacce dabba na samun irin wannan wahayi
(shi masana kimiyya ke kira da instinct). Shi kudan zuma ana samun sa ko’ina
cikin duniya idan banda kananan tsibirai da ke cikin teku, sassa masu kankara
da a kololuwar manyan tsaunuka. Haka nan kamar yadda ayar ta nuna suna gina
gidajensu a cikin muhallan da mutane ke zaune. Akwai a kalla jinsuna 20,000 na
kudan zuma kuma suna da banbance-banbance saboda akwai masu launin baki, ruwan
dorawa,shudi, kore da sauransu. Gidajensu na kasancewa a tsare tamkar unguwa da
mutane ke zaune. A cikin shuri na kudan zuma akwai bangarori daban-daban misali
akwai fadar sarauniya, gidajen maza da bangaren mata, sannan akwai rumbuna na
ajiye zuma, da wurin saka kwai da dakunan jarirai. A sheka guda ta kudan zuma
akan sami kudajen zuma 80,000 ko fiye, kuma a tsarin zamantakewar su sun kasu
kashi uku. Wato akwi sarauniya, ma’aikata (wadanda mata ne) da kuma mazaje.
Sarauniya ita kadai ke haihuwa a cikinsu, a rana guda tana iya
saka kwi 1500 kuma tsawon ran ta ya na kaiwa daga shekara1-3. A siffa ta
banbanta da duk sauran kudan zuma, kuma ta kan sadu da maza shida ko fiye da
haka. Daga wannan saduwa ba ta sake saduwa da namiji tsawon rayuwarta, amma
dukkan maniyyin da suka dura mata tana tara shi cikin wata ‘yar jaka a cikin
cikinta. Lokaci-lokaci sai ta rika amfani da shi wajen saka kwai kuma ita ce ke
da alhakin zabar ma kwai irin jinsin da zai kasance (wato ya zama sarauniya
irinta ko mace ko kuma namiji). Ta na yin haka ne sakamakon wajen da ta ajiye kwai,
misali idan wadanda zasu zama sarauniya ne sai ta saka kwan su a cikin wasu
kebabbun akusa da aka gina su a saman shekar kuma a rika basu wani kebabben
abinci (Royal jelly) har zuwa lokacin da za’a kyankyashe su. Duk irin wadannan
kwayaye na zama sarauniya kuma daga kyankyasarsu zuwa balagarsu kwana 16 ne. Su
kuma ma’aikata tana saka kwansu ne a wasu akusa da aka gina a dandakwaryar
kasa, sannan ana basu wancan kebabben abinci tsawon kwana biyu ne kacal.
Ma’aikata na balaga ne bayan kwanaki 21 da kyankyasa. Maza kuma na balaga ne
bayan kwana 24. Aya ta gaba ta ci gaba da cewa
Q16:69” Sannan ki ci daga dukkan ‘yayan itace”
Kamar yadda na fada a baya kudan zuma na da tsarin kaso uku na
sarauniya, mata da maza kuma mata sune ma’aikata waoto duk wata hidima ta shuri
da ta shafi farautar abinci da kula da rayuwa sune ke aiwatar da ita. A wannan
aya sai Allah yayi amfani da wakilin suna na mace (feminine gender) wajen cewa
“ki ci” wato anan da matayen kuda zuma Allah ke magana domin dai sune ke gina
shekar kanta wajen tsara dakuna da tsabtace su. Abincin kudan zuma shine ruwa
mai zaki da ake samu cikin furanni. Kowanne jinsi na kudan zuma akwai akwai
irin furannin da suke ci, wannan shi yasa ake samun ruwan zumar da suke samarwa
yake banbanta. Akwai zuma farar saka, ruwan kasa, ja, ruwan dorawa da sauransu.
Mataen kuda zuma su ne ki fita don nemo irin wannan ruwa su rika tara shi cikin
wani holoko da ke cikin makogwaronta idan ta dawo sheka sai masu adana abinci
su tare ta sai ta juye musu su kuma sai su kai shi cikin rumbuna don
ajiya. Idan rumbun ya cika sai su shafa masa wani danko da suke samarwa daga
jikinsu don like rumbun kada iska ta shiga. Wani gagarumin aiki da kudan zuma
ke yi sakamakon yawo daga wannan fure zuwa wancan a yayin farautar fure shine
na barbarar tsirrai. Wato a yayin da kudan zuma ta sauka kan wani fure tana
zukar ruwan sukari da ke ciki, to kafafuwanta na kwasar kwayoyin maniyyi na
wannan fulawa. Idan tayi gaba kuma ta sauka a wani furen da yake mace sai
kwayoyin maniyyin su makale a kai, ta haka ta barbari wadannan furanni. A yanzu
masana ilimin kwari na cewa sakamakon wannan Barbara da kudan zuma ke yi yana
samar da akalla kudin da ya kai kimanin dala biliyan 20. Ayar ta ci gaba da
cewa
Q16:69” Saboda haka ki shiga hanyoyin ubangijin ki, suna
horarru”
Hanyoyin da kudan zuma ke bi wajen sadarwa a junansu ko zuwa
farautar abinci akwai matukar gwaninta da tsari. Da farko dai ma’aikata a
farkon rayuwarsu ana fita dasu daga cikin shuri don koya nusu hanyiyin da ake
bi wajen zuwa neman fure da gane hanyar dawowa gida. Suna amfani da rana wajen
gane lokaci da kuma nahiyoyi, daga kofar shurin sai su kalli rana don su gane a
nahiyar da take, don haka duk nisan da zasu yi suna amfani da wannan kusurwa da
rana take don gane hanyar dawowa gida. To idan lokacin damina ne ko na hunturu
da wani lokacin xaka ga rana ta bace cikin hadari ko hazo fa? Allah cikin
hikimarsa sai ya hore ma idanuwansu iya ganin zaruruwan
ultravoilets dake fitowa daga rana, wadannan zaruruwa na iya ratsa
kusan komai ba kamar hasken rana ba. Ta amfani da gane kusurwowin da wadannan
zaruruwa suka fada, da haddace su sai kawai su kama gabansu suna la’akarida su
har su je inda zasu su dawo, tamkar yadda masu jirgin ruwa ke amfani da compass
wajen gane nahiya. Wani abin mamakin kuma shine yayin da wani kudan zuma ya
gano wani waje mai furen da ake nema don tsari na adalci maimakon a saka ta
gaba ta koma ta nuna wurin sai ta yi musu kwatance. Yadda take kwatancen kuma
shine sai suyi da’ira su kewaye ta, ita kuma sai ta fara rawa da zarya da
kewaye wadanda kowanne cikin irin abinda take yi yana da labarin da ya ke
bayarwa. Kamar yadda kowa ya sani cewa duniya da’ira ce da ke da kusurwa 360,
don haka wannan da’ira tasu ta zama kamar taswira. Sai ta fara kewayen da’irar
wanda ke sa su rika shakar irin kanshin furen da ta samo, duk sanda ta kewayo
sai ta ratsa ta tsakiya ta nufi daya gefen. Saitin layin da ta ratsa zai sanar
dasu nahiyar kusurwar da ta je, sannan iya zagayenta na nufin iya nisan wajen
daga shurinsu. Idan tayi zarya sama kuma na nufin wajen abincin da ta gano yana
sashen da rana take, amma idan tayi zarya kasa kuma na nufin sashen yana sashen
da rana ta bari. Wadanda suka kewaye ta suna kallon ta ba wai zuru kurum suke
yi mata ba domin su hardace abinda ta ke koya musu sai su rika kwaikwayon duk
irin rawa da motsin da ta tayi. Suna kammalawa sai suyi waje “duuu..” don isa
wannan waje.
Wani aikin kuma da ma’aikata ke yi shine na kokarin tsabtace da
kula da muhallinsu ta hanyar share shi da kuma samar da daidaiton yanayin zafi
ko sanyi (Temperature) cikin shurin. Misali idan a lokacin zafi ne
sukan yi kamar wata ‘yar rumfa suyi ta karkada fuka-fukansu a matsayin fanka
domin su kori iska mai zafi don shurin ya huce haka kuma a lokacin hunturu suna
yin cincirindo su zama kamar bargo sai su lullube jarirai da kwayayensu, su
kuma kasancewa a waje guda suna samun dumin juna. A kowanne lokaci suna kokarin
daidaita yanayin sheka ya kasance baya gaza ko wuce mizanin 33.9 a ma’aunin
zafi na centigrade, don shine iya dumin da kwayaye ke bukata kafin su
kyankyashe. A cikin ayar dai sai Allah ya ce
Q16:69” Wani abin sha yana fita daga cikunanta, mai sabawar
launuka, a cikinsa akwai wata warkewa ga mutane”
Sakamakon banbance-banbance na ire-iren furannin da suke ci,
shine ya samar da launuka daban-daban na ruwan zuma. Ana samun fara ko ruwan
dorawa ko ruwan kasa da sauransu. Dandano kalilan ke kai zuma wajen zaki da
dadi, wannan ya sa Mutane suka samar da hanyoyi da dama na sarrafa zuma a
matsayin abin sha ko ci. Babu wani abin sha da kan iya dadewa ba tare da an
saka masa sindarin hana lalacewa ba kamar zuma, don ta kan kai shekaru a aje ba
tare da ta lalace ba. Wannan ya biyo bayan kasancewar a cikin zuma akwai
sinadarin da ke yaki da kwayoyin cuta (Wato Antibiotics) irinsu bacteria da ke
saka funfuna ko lalacewar abinci kai har ma da kwayar Virus. Kwayoyin cuta na
bacteria da virus sune ke haddasa kusan kashi casa’in na cututtukan da ke
duniya. A yanzu ana amfani da zuma wajen yaki da cututtuka irinsu na kwanji,
jijiyoyi da abin da ya shafi garkuwar jiki, ina ganin da masana ilimin
magunguna zasu zurfafa bincike watakila su gano hanyar magance kanjanmau.
Zuma na da dafi wanda take amfani dashi don kariyar kanta daga
abokan gaba, a duk lokacin da wata halitta take barazana gareta to sai su buga kugen
yaki su far mata da harbi har sai sun hallaka ta ko sun koreta. Shi kansa
wannan dafi nata, masana harkokin harhada magunguna na zakulo shi don su cire
wani sinadari da ke maganin ko wane irin dafi. Daga karshe sai Allah ya ce
Q16:69” Lallai ne a cikin wannan, Hakika akwai ayoyi ga mutane
wadanda suke yin tunani”
A cikin ayoyi biyu kacal Allah ya dunkule mana irin ilimin
rayuwar kudan zuma, wanda ke cike da bayanai na gwaninta da suke nuna isa da
kwarewa ta Allah. Kuma kamar yadda na fada a baya babu wani kwaro da masana
suka yi bincike a kansa kamar kudan zuma domin an rubuta daruruwan littattafai
da kasidu a kansa. Allah a cikin Qur’ani ko da yaushe yana jan hankalin mu da
mu yi tunani, domin dai tunani shine ya banbanta mu da sauran dabbobi amma kash
sai dai a yau al’ummar musulmi mune koma baya wajen bincike da nazari wanda
shine irin tunanin da Allah ke ta umartar mu. Allah ya sa mu gane domin mu koma
kan matsayin mu na ja gaba tun asali.
Comments
Post a Comment