LANTAR-MAGANADISU
Wani muhimmin al'amari da yake shima babban
ginshiki ne wanda Allah ya samar domin tafiyar da rayuwa ta abubuwa masu rai da
marasa rai, shine lantarki da maganadisu. A cikin surayul yasin Allah yana cewa
Q36:36" Tsarki ya tabbata ga Allah wanda
ya halicci nau'i bibbiyu na abinda ke fita daga kasa, da su kansu (mutane) da
ma abinda ba su sani ba"
Ya halicci dukkannin halittu a tsari mai
biyu-biyu, wato babu wata halitta da bata da kishiya. Ba ma halitta da muka
sani ba Allah na cewa a cikin abubuwa da ya halitta wadanda ma bamu sani
ba duk wannan tsari na bibbiyu suke bi. Hikimar wannan shine domin Allah ya
tabbatar wa kowa cewa shi kadai ne tilo da bashi da abokin tarayya.
Lantarki da maganadisu suna cikin hikimar
Allah na tsara abubuwa bibbiyu, kuma suna daga cikin farkon abubuwan da Allah
yafara halitta, domin dai bayan samar da kwayar zarra wadda ita ce bulon ginin
kowacce halitta mai rai da mara rai, lantarki da maganadisu sune ginshikan da
ke dauke da kwayar zarra. Kowacce kwayar zarra ta kasance wani dan dunkule ne
da yafi kankanta cikin halitta, cikin wanan kwaya zarra akwai kuma wasu kananan
abuwa da suka tattaru suka yi ta. Tamkar dai wata 'yar da'ira ce dake da
tsakiyarta cunkushe da wasu kananan abubuwa da ake kira protons (wato masu
dauke da cajin lantarki mai karbar wuta + positive charge) sannan kewaye da
wannan tsakiya akwai wasu abubuwan da ke kewaya tsakiyar a matsanancin gudu su
ake kira da electrons (wato su kuma suna da cajin lantarki mai bada wuta -
negative charge). Kasancewar kwayoyin zarra suke tattaruwa su yi
halittu masu rai da mara sa rai, ya sa cewa sammai da kassai na cike da cajin
lantarkin nan guda biyu. Wannan caji na lantarki shi ke bada damar kwayoyin
zarra su yi cudanya da juna. Idan kwayar zarra na da cajin lantarki mai
karbar wuta (wato negative -) fiye da cajin da ke bada wuta (wato positive +)
sai ace wannan kwayar zarra ta yi shirin bada wuta, amma idan cajin bada wuta
yafi cajin karbar wuta sai a ce ta yi shirin karbar wuta. Amma yayin da cajin
suka yi kunnen doki sai a ce babu caji kenan ko cajin na tsaye (static
electricity). Misali idan ka gurza abubuwa daban-daban guda biyu, kamar mataji
na shace kai a cikin gashin kanka wasu daga cikin cajin lantarki mai
karbar wuta na cikin gashin kanka sukan yi tsalle su dafe matajin don haka shi
matajin, saboda karuwar cajin da ya samu daga gashin kanka, ya zama mai cajin
karbar wuta amma shi gashin kanka kuma ya zama caji mai bada wuta domin ya rasa
wani daga cikin cajin sa. A duk lokacin da abubuwa guda biyu ke da mabanbantan
cajin lantarki na karbar wuta da bada ita ,to wadanan abubuwa na zawarcin
juna amma idan cajin su iri daya ne to suna guje ma juna. Idan
abubuwan masu zawarcin juna suka sami saduwa har ta kai cajin
lantarki daga daya zuwa daya ya samu, to idan aka sami gudanar wannan caji babu
kakkautawa ta cikin wani abu (conductor-wato abubuwa dake barin lantarki ya
ratsa ta cikin su ba tare da tare shi ba) sai ya haifar da gudanar lantarki
(Current flow) amma idan abu ya hana lantarki wucewa shine ake kira da
insulator. A duk inda cajin lantarki yake to yana samar da wani sarari kewaye
da wajen da lantarkin ke motsi (electric field) shi kuma wannan sarari na
lantarki sai ya haifar da sararin maganadisu (magnetic field). Haka kuma shima
duk inda aka sami sararin maganadisu yana samar da sararin lantarki. Wannan
auratayya tsakanin sararin lantarki da maganadisu sai ta haifar da wani sararin
na lantar-maganadisu (electromagnetic field). Rana ita ce wurin da ya fi
kowanne samar da wanan sarari na lantar-maganadisu kuma duk zaruruwan dake fita
daga cikin rana igiyar lantar-maganadisu (electromagnetic waves) ke iso mana da
su doron duniya, domin babu wani abu da ke da saurin wannan igiya a cikin
halittun subhana wadanda muka sani a yanzu. Alaka tsakanin lantarki da
maganadisu an fara gano ta ne cikin shekarar 1819 yayin da wani baturen Danmak
ya gano cewa allurar maganadisu da ake amfani da ita wajen gane turken nahiyar
arewacin duniya (North magnetic pole) tana iya motsawa duk lokacin da aka kawo
wayar lantarki kusa da ita. Bayan wannan kuma sai wani mutumin faransa ya gano
cewa wayoyin lantarki guda biyu suna mu'amala tamkar yadda mayen karfe guda
biyu ke yi yayin da aka nemi hadasu. Sannan kuma shahararren masanin kimiyya na
Birtaniya wato Micheal Faraday shima ya gano cewa za'a iya saka lantarki ya
motsa ba tare da amfani da batir ba idan idan aka motsa maganadisu a wurin. A
karshe kuma sai bajamushen nan Heinrich Hertz cikin shekarar 1887 ya gano cewa
ai za'a iya samar da igiyar lantar-maganadisu ta hanyar amfani da lantarki
wanda wannan yana daga cikin gagaruman abubuwan da Dan Adam ya gano da ya canza
duniya har abada domin ya bada damar samar da rediyo, talabijin, rada, nau'ra
mai kwakwalwa da sauran hanyoyin sadarwa. Shine yasa muke iya saurararon
shirye-shirye na radio, talabijin, komfuta da waya kai tsaye daga sassan da ake
watsa su tamkar muna wurin saboda igiyar lantar-maganadisu na tafiyar mil
186,000 a sakan daya yayin da nisan zagayen kwallon duniyarmu (Earth
circumference) kilomita 40,000 ne kawai. A can cikin kwallon duniyarmu akwai
wuta ta narkakken karfe da ke ci gagga-gagga, Allah na nuna mana irin wannan
wuta lokaci-lokaci yayin aman wutar dutse (volcanic eruotions) ko girgizar
kasa, wannan wuta ta haifar da sararin maganadisu a duniya. Saboda duniya
na juyawa ya haifar da juwayar wannan narkaken karfe cikin tumbin duniya,
shi yasa ake samun canzawar turken maganadisun duniya (magnetic poles) dake
kusurwar kudanci da arewacin duniya (north and south magnetic poles). Wannan
maganadisu kansa yana daga cikin rundunonin da ke kare doron kasa da halittu,
domin shi wannan sararrin maganadisu da ya kewaye duniya yana hana wasu
muggan zaruruwan sama'u (cosmic rays) da kuma guguwar rana (solar winds)
daga isowa doron kasa kai tsaye. Ita wanan guguwa ta rana tana koro wasu
abubuwa masu matsanancin cajin lantarki (charged particles) da kan iya kone
duniya gaba daya, amma sai wannan sararin maganadisu na duniya ya tare su ya
mayar da su sama. Yan kalilan daga cikin su da ke kubcewa su iso doron kasa su
ke haifar lalacewar yanayin sadarwa wani lokaci ko kuma wani matsanancin haske
mai launuka da ke faruwa a doron duniya na kudu da arewa (wato polar lights ko
aurora).Wadannan turken maganadisu na duniya daya yana kusa da garin Greenland
can arewacin turai dayan kuma yana cikin hamadar kankara ta
Antarctica. Kafin gano amfanin lantar-maganadisu, mutanen da na amfani da
turken maganadisu na arewacin duniya ta amfani da allurar mayen karfe
(compass)wajen gane nahiyar arewa da masu tafiya a tudu da teku ke amfani da
ita. Wannan na tabbatar da ayar da ke cewa
Q22: 65
"Shin ba ku gani ba cewa Allah ya hore maku (ku mutane) duk abin da ke
duniya"

Comments
Post a Comment