RARRABEWAR NAHIYOYIN DUNIYA

 

Kimanin shekaru miliyan dari biyu das u ka wuce nahiyoyin duniya sun kasance a dunkule wuri guda kafin su fara rarrabewa, abinda ya samar da nahiyoyi shida da mu ke da su a yanzu. Rarrabewar nahiyoyi ya haifar da samuwar jerin carbin manyan duwatsu kusan a kowacce nahiya. An sami jerin carbin duwatsun Cordilleran a nahiyar Arewacin Amurka da kuma jerin duwatsun Andes a kudancin Amurka. Motsin Indiya wanda ya ci zango mai nisa ya haifar da jerin duwatsun Himalayas, jerin carbi mafi girma a duwatsun duniya inda ma ake da tsauni mafi tsawo (Mt. Everest). An sami jerin duwatsun  Alpine a Turai sakamakon jijjigar kudu da arewa tsakanin Afurka da Turai wanda kuma ya haifar da tekun Bahar Rum (Meditarranean sea). An sami jerin duwatsun Atlas a arewacin Afurka. Ta haka wadannan duwatsu su ka zama ginshikan da su ke rike da nahiyoyin kamar yadda Allah ya ce cikin suratul Naba’i:

“Da duwatsu turaka (ga rike kasa)”

Wasu da ga cikin hujjojin da su ka tabbatar da wannan al’amari a kimiyance su ne: An sami dabbobi da su ke a sassa na duniya wadanda ba suda wa ta hanya da za su iya ketara tekuna, sai dai idan sun kasance a bangarorin  kasa kafin rarrabewar nahiyoyin. Akwai tsirrai irin na kurmi da aka samu a wuraren kankara, da kuma hujjar cewa akwai kasusuwan kakannin kadangare da aka tono a Antaktika binne can karkashin kankara wanda ke tabbatar da cewa sun rayu a wajen kafin nahiyar ta daskare. Haka kuma an sani kasusuwan kifaye a binne cikin Saharar Afurka, wadda shi ma ke nu na a da can wurin akwai ruwa. Binciken masana kimiyya na maganadisun karkashin kasa ya nuna cewa nahiyoyi sun marmatsa, saboda alluran maganadisu a koda yaushe na fuskantar doron duniya da ke Arewa (North Magnetic Pole) amma bayan nahiyoyi sun marmatsa sai wadannan allurai ke fuskantar sashen da nahiyoyi suka bi bayan ballewarsu maimakon arewacin. Masana sun tabbatar da cewa har yanzu nahiyoyi na motsin a kalla inci daya a duk shekara, wanda yasa ake hasashen cewa zirin California dake Amurka zai balle kuma tekun Atalantika zai kara fadada nan da wasu shekaru. 

KWANA NA HUDU (CENEZOIC ERA)

Wannan shi ne kwana na karshe da Allah ya yi halitta cikin kwanaki shida da ya yi halittar sammai da kasa, kuma kwanan karshe a cikin kwanaki hudun da ya yi halitta a duniya. Wannan lokaci ya fara ne kusan shekaru miliyan 75 da su ka wuce. A cikin shekaru miliyan 500 da halittun dabbobi su ka habaka a duniya an sami faruwar gagaruman Annoba wadda ke halaka dukkan halittu na zamanin da su ka auku. Iri-irin wannan annoba ta auku sau biyar.

 

-Ta farko ita ce wadda ta auku kusan shekaru miilyan 438 da su ka wuce. Wannan annoba ta halaka kusan kashi 85 na wannan zamani

 

-Ta biyu ta auku a shekara miliyan 367 da su ka wuce wadda ta hallaka kashi 82 na halittu.

 

-Ta uku itace wadda ta fi kowcce annoba tsanani a cikin dukkan annobar da ta taba aukuwa. Ta auku a shekara ta miliyan 245 ya yin da ta kusa hallakar da dukkan halittun wannnan zamani domin kashi 96 na halittu sun mutu a wannan zamani. Bayan wannan annoba ne aka fara samun sabbin halittu irin na zamani.

 

-Ta hudu itace wadda ta auku a shekara ta miliyan 208, ta kuma hallaka kashi 76 na halittu.

 

-Ta biyar kuma ita ce wadda ta auku a shekara ta miliyan 65, wadda ta halaka kashi 76 na halittu. A wannan zamani ne kakannin kadangare su ka halaka, wadannan halittu sun kasance mafi girma da yawa a tarihin dabbobi. Masana da dama sun yarda cewa dalilin aukuwar wannan annoba shi ne sakamakon fadowar wani katon dutse da ga cikin irin ragowar duwatsun da aka yi duniyoyin da ke cikin rukunin tauraronmu. Irin wadannan duwatsu (Meteorites) su na yawo a sararin samaniya, wasunsu na kewaya rana kamar yadda duniyoyin mu ke yi. Wannan dutse da ya fado duniya a wannan lokaci ya kai fadin kano zuwa kaduna (200 km). Yayin da ya fado ya haifar da wani gagarumin rami a zirin Yucatan da ke kasar Mexico a yanzu, ya tayar da gagarumar kura wadda tayi sama ta turnike sararin duniya yadda sai da aka yi watanni hasken rana baya isowa duniya. Sakamakon haka ya sa dukkan tsirrai su ka mace saboda da hasken rana ne su ke sarrafa abincinsu. Rashin tsirrai kuma ya jawo mutuwar dabbobi da yawa. Da ga burbushin halittu na wannan zamani aka sami sabbin halittu. A wannan lokaci, bayan waccan annoba aka fara samun dabbobi masu mahaifa (Placental mammals). Manyan dabbobi masu rarrafe (Reptiles) su ka kare. Kananan dabbobi irinsu kunkuru da kada sun tsira. Bayan shekaru miliyan goma da wannan annoba sai tsirrai masu fure (Flowering Plants) su ka habaka. Biran farko da Gwaggo sun bayyana a wuraren Burma a kudancin Asiya. Kakannin giwar yanzu (Mammoth), Karkanda, Doki, Alade da Shanu su ma sun bayyana wajen shekaru miliyan 38 da su ka wuce. An sami janyewar dazuzzukan manyan bishiyoyi wanda ya haifar da habakar ciyayi, wanda shi kuma ya taimakawa ci gaban dabbobi masu kofato. A Afurka halittu masu siffofin birai amma masu tafiya kan kafafu biyu sun bayyana kuma su ka fara watsuwa zuwa nahiyoyin Asiya da turai (Pro-consul).

A wuraren shekaru miliyan goma aka fara samun kakannin Dan Adam da ga burbushin wadancan halittu. Kankara ta lullube yawancin Turai da Amurka, Antaktika da ma bangarorin Afurka. Narkewar kankara lokaci-lokaci ta haifar da karuwar tekuna. A wannan lokaci ne mutanen farko su ka samu a tsakanin shekaru miliyan hudu da su ka wuce. Mutum shi ne ya zama cikamakin halitta, domin ya zo ne bayan kusan kashi 99 na halittu sun samu kamar yadda Allah ya ce mana cikin suratul Insan:

Q76:1 “Lallai ne wa ta mudda ta zamani (mai tsawo) ta zo a kan mutum, bai kasance komai ba wanda ake amba ta”

Mutum ya kasance halitta ta karshe kuma ya zama mafifici cikin dukkan halittun da Allah ya halitta. Rarrabewar nahiyoyi (Continental Drift) zuwa nahiyoyi shida wato Afurka, Asiya, Turai, Amurka ta kudu da arewa, Australiya da Antaktika, ya bada damar warwatsuwar halitta iri guda zuwa bangarorin duniya daban-daban. Kuma ya ba su damar bunkasa daidai da yanayin nahiyoyinsu. A da can jinsuna daban-daban na ketara nahiyoyi kasancewar akwai gadoji da Allah ya yi, misali akwai wa ta gada tsakanin nahiyoyin Asiya da Turai zuwa Amurka (Bering Strait). Akwai kuma wani zirin kasar da ya hada nahiyar Afurka da Turai (Gibraltar strait). Bayan rarrabewar nahiyoyi kuma, abubuwa irinsu sahara, koguna da manyan tsaunuka sun taimaka wajen kebance wasu halittu da ga cudanya da barazanar manya dabbobi. Misali a Australiya da ta zama gefe guda ita kadai, ya sa akwai halittu mafi tsufa na dabbobi masu bada nono a wannan nahiya ya yin da na wasu nahiyoyin su ka kare. Samuwar manyan teku na irinsu Pacific wanda tsawonsa da ga kudu zuwa arewa kilomita 15,000 ne, sannan fadinsa da ga gabas zuwa yamma kilomita 17,000 ne, ya kebance nahiyoyi da halittu ta yadda ko dabbobin ruwa ba sa iya ratsa gaba zuwa gaba. Sannan manyan tsaunuka sun zama tamkar ganuwa tsakanin nahiya guda, misali jerin carbin Himalayas da ya zama ganuwa tsakanin arewacin Asiya da gabashi. Yanayi shi ma ya yi gagarumin tasiri wajen banbance jinsuna, akwai wuraren kurmi da ke da zafi sosai da dazuzzuka (Tropical) don haka dabbobin da ke nan su kan zubar da gashin jikinsu wasu ma gaba dayan gashin su ke zubarwa, kamar su giwa da dorinar ruwa. Amma wadanda ke wuraren sanyi su kuma gasusuwansu na habaka domin kariya da ga sanyi, kamar su malu da kakannin giwar yanzu (Mammoth). Irin wannan banbancin yanayi shi ya fara kawo banbancin launin fata a jinsin Dan Adam, wato mutanen da su ka zauna a sassa masu zafi sai su ka rika yin duhu amma wadanda ke sanyi kuma fatunsu su ka kara haske.

 

Comments

Popular posts from this blog

BAKAR TAURARUWA (BLACK HOLES)

RUKUNIN TAURARONMU-RANA

TSUNTSAYE