RAI/RUHI DA MUTUWA
Menene
Rai ko Ruhi? Wannan tambaya ce da ta shige ma Dan Adam duhu tun farkon
halittarsa. Daidaikun mutane da Addinai da dama sun yi iya kokarinsu wajen
ganin sun gano bakin zaren wajen fahimtar rai. Amma babu wani addini da ya iya
kawo cikakken bayani kafin zuwan musulunci. Kafiran Makka, Yahudawa da Nasara
na kalubalantar Annabi da ya kawo musu mu'ujiza kamar yadda Allah ya bamu
labari cikin Suratul Ankabut
Q29:50
"Kuma su ka ce "Don me ba'a saukar masa da ayoyi (na mu'ujiza) daga
ubangijinsa"
Sai
Allah ya ba su amsa a cikin aya ta gaba inda ya ce
Q29:51"
Shin bai ishe su ba cewa lallai mu, mun saukar da littafi a kanka, ana karanta
shi a kansu"
Allah
na tabbatar mana da cewa Annabi bai zo da wata mu'ujiza face Qurani ba, domin
dai shi ummiyi ne wato bai iya karatu ba ballantana rubutu amma ya zo da
littafin da ke kunshe da ilimi na kowanne fanni wanda ba'a taba jin irinsa ba,
kuma ba za'a taba ji ba. An saukar da wannan littafi a guggutsure tsawon
shekaru 23 amma babu wata aya guda da aka saukar a shekarar farko a Makka wadda
zata ci karo da wata ayar da aka saukar bayan shekaru ashirin a madina. Kuma
kama daga fannin zamantakewa zuwa nahawu, kimiyya, tarihin mutum da asalin
halitta babu inda aka bari a baya. Allah y ace
Q6:38 “Ba mu yi sakacin barin komai ba
cikin littafi”
A cikin karni na bakwai sanda aka saukar da
littafin, duniya na cikin duhun jahilci domin dai addinan yahudu da nasara sun
gurbace an yi watsi da ainihin koyarwar littatafan. Amma kasancewar duk da haka
babu wanda yafi Yahudu da Nasara ilimi a wannan zamani sai suka fara
kalubalantar Annabi da tambayoyi na ilimi. Akwai jerin tambayoyi, musamman
guda uku da suka ce in dai shi annabi ne lallai zai iya ba su amsa saboda sun
dade su na son amsoshin wadannan tambayoyi kuma an ce musu sabon annabin da zai
zo shine kadai zai iya basu cikakkiyar amsa. Lokacin da su ka zo su ka mika
wadannan tambayoyi guda uku ga annabi sai ya ce musu su dawo gobe zai ba su
amsa. Kasancewar Allah na son mu fahimci mahimmancin sa a rayuwar mu kuma ya
nuna mana cewa Annabawa ma na iya yin kuskure ko da yake kuskuren su ba na
zunubi ba ne, kuma ba sa gushewa sai Allah ya kautar da su daga wannan kure.
Dalilin haka sai ya ki sanar da annabi amsoshin tambayoyin har tsawon
makonni ta yadda kafirai suka rika zunden annabi suna cewa ai makaryaci ne.
Dalilin wannan ne Allah ya ja masa kunne a cikin suratul Kahaf
Q18:23
" Kada ka ce a game da komai "lallai ne gobe zan yi"
Daya
daga cikin tambayoyin da su ka yi ita ce, Menene Rai ko Ruhi? Cikin suratul
Isra sai Allah ya ba da amsar
Q17:85"Su
na tambayarka game da ruhi ka ce "Ruhi daga al'amarin ubangijina ne. kuma
ba a ba ku (komai) ba daga ilimi face kadan"
Tun
da Allah ya halicci duniya zuwa yanzu babu wani mahaluki da zai ce ya
fahimci yadda rai ya ke domin dai iliminsa kadan ne Allah ya sanar da mu. Shi
rai wani kebabben muhalli ne na Allah domin shine sirrin rayuwa kuma shi ne ke
tabbatar da cewa babu wani mahalicci sai Allah. Na farko dai daga wajen Allah
rai ya samo asali kamar yadda ya bamu labari cikin suratul Hijiri yayin da
Allah ya shirya halitta a doron kasa kuma ya ke bai wa mala'iku labari
cewa
Q15:29"
To idan na daidaita shi (wato Adam) kuma na hura Ruhina a cikinsa to ku fadi
gareshi kuna masu sujada"
Ruhi
ya samo asalinsa daga ubangiji domin ruhin ubangiji da ya hura ga Adam shine
asalin rayuwa a wannan duniya tamu, haka kuma kowanne mahaluki ba ya samuwa sai
daga wannan ruhi na ubangiji kamar yadda ya ce mana cikin suratul Sajda
Q32:8-9" Sannan
ya sanya yayansa daga wani asali na wani ruwa walakantacce. Sannan ya
daidaita shi kuma ya hura a cikinsa daga ruhinsa , kuma ya sanya muku ji
da gani da zukata. Godiyarku kadan ce kwarai"
Don
haka kowannen mu ba zai iya samuwa ba sai daga wannan ruhi da Allah ke busawa
daga gareshi, wannan shi ya sa ruhi ya fi karfin duk wadansu hanyoyi na sadarwa
da Allah ya hore mana, domin ba ma iya jinsa, dandanarsa, ganinsa ballantana ma
mu taba shi. Kawai dai muna iya sanin yana nan ko kuma baya nan ta
hanyoyin gane abu rayayye da matacce. Duk inda mai rai yake sai mu san akwai
rai kuma duk inda matacce ya ke mun san cewa rai ya fita. Ilimin ruhi kalilan
ne Allah ya sanar da mu. Allah ya kalubalanci dukkan halittu da cewa wanda
duk yace akwai Allah bayan Allah to hanya guda daya tilo da za'a banbance
allolin karya da Allah na gaske shine kamar yadda ya ce mana cikin Suratul Hajj
Q22:73"
Ya ku mutane ga wani misali, sai ku saurara zuwa gareshi, lallai wadanda kuke
kira baicin Allah, ba za su iya halitta kuda ba, ko da sun tattaru (da taimakon
juna) domin hakan"
Don
haka idan da wani wanda zai iya halittar kuda to bismillah, kuma in har ya iya
yi, to za mu sallama masa, amma babu wanda zai iya, domin Allah ya boye wannan
ilimi domin ya tabbatar wa masu imani cewa shi kadai ne “iIah”. Masana kimiyya
tsawon shekaru sun yi iya kokarinsu wajen samar da halitta mai rai daga abubuwa
mara sa rai amma sun kasa kamar yadda suka tabbatar cikin kundin nazarin
kimiyyar halittar rayuwa (Encyclopaedia of Biological science) cewa "Dukkan
wani kokari na samar da halitta mai rai kai ko ma wani sashe na halitta mai rai
daga abubuwa marasa rai ta hanyar binciken kimiyya ya ci tura" Cikin
fitattun masana kimiyya da su ka bata shekaru wajen binciken sama da halitta
mai rai, akwai Stanley Miller wanda bayan gazawa ga abinda y ace “Hakika gano
yadda rai ya samo asali ya kasance wata matsala da tabbata gagararriya fiye da
yadda ni da mutane da dama su ka dauka”. Haka nan Simon Conway shi ma cewa ya
yi “Hakika an kasa samar da rai a dakin bincike, kuma babu wata alama da cewa
za’a iya yi nan gaba…samuwar rai wani al’amari ne gagara misali, sai dai kawai
mu ce samuwar rai mu’ujiza ce”. Abokin binciken Stanley Miller, wato Francis
Crick wanda su ka yi shekaru gwammai na wannan bincike shi ma cewa ya yi “Duk
wani mai fadar gaskiya, da yak e da ilahirin ilimin da muke da shi a yanzu, zai
sallama cewa hakika yadda rai ya samu a doron kasa abu ne da kawai sai dai a
kira shi da mu’ujiza” Don haka duk yadda mu ka kai ga ilimi ba zamu iya gane
sirrin rai ko ruhi ba face dan kalilan da Allah ya sanar da mu. Rai abokin tagwaitar mutuwa ne, saboda duk
lokacin da babu guda akwai gudan. Shi kuma ruhi tun sanda Allah ya fara
halittarsa yana nan a raye sai dai kawai yana bayyana ne a matsayin rai a
lokacin da aka hada shi da jiki amma da zarar an cire shi daga jiki
sai ruhin ya kasance a matsayin mutuwa. Shi yasa Allah ya ce mana cikin suratul
Baqara
Q2:28"
Ya ya kuke kafirta da Allah, alhali kun kasance matattu sai ya rayar
da ku, sannan ya sanya ku ku mutu sai ya sake rayar daku, kuma
gare shi zaku koma"
Wato
dukkan mu zamu fuskanci mutuwa biyu da rayuwa biyu. Domin bayan Allah ya
halicci dukkan rayuka kuma ya shaidar da su kan mulkinsa sun kasance a yanayi
na mutuwa kafin a hada kowanne ruhi da gangar jikinsa (mutuwar farko). Da zarar
jiki ya sami ruhi sai ya zama rayaye (rayuwar farko) sannu a hankali kuma sai
kowanne mai rai ya dandani mutuwa (mutuwa ta biyu) sannan a lahira kuma ranar
tashin kiyama sai a busa wa kowa rai (rayuwa ta biyu kenan). Saboda irin kauna
da Allah ke wa bayinsa bai bar mu cikin duhu ba don haka don yana son mu
fahimci rayuwa da mutuwa sai ya tsara mu kamar haka
Q39:42
"Allah ne ke karbar rayuka a lokacin mutuwarsu, wadanada ba su mutu ba
kuma (ya karba ) a cikin barcinsu. Sannan ya rike wanda ya hukunta mutuwa a
kansu, kuma ya saki ragowar zuwa ga ajali ambatacce. Lallai a cikin wannan
akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani"
Kamar
yadda bahaushe ne ke cewa "Barci kanin mutuwa". Wato a lokacin
kowanne barci ana yin 'yar karamar mutuwa ne don Allah na karbar rai ne sai
barci ya kwashe ka. Wanda duk lokacin barcinsa ya dace da na ajalinsa shi ke
nan babu tashi sai dai ya yi tazarce, amma wanda ke da sauran kwana sai a mayar
masa da ran sa ya farka. Shi barci babu wanda zai ce ya san takamaimai lokacin
da zai dauke mutum sai dai kawai ya sace ka, kamar yadda mutuwa ita ma bata
sallama sai dai ta zo bagatatan. Haka nan ita ma farkawa baka sanin zuwanta sai
dai wani abu ya farkar da kai kwatsam. Saboda haka barci da farkawa abubuwa ne
guda biyu da Allah ya halitta a jikin mu don su tabbatar mana da cewa lallai
akwai mutuwa da tashin kiyama wato barci tamkar mutuwa haka nan farkawa tamkar
tashin kiyama. Allah y aba mu labarin cewa
Q36:52 “Su ka ce “Ya bonenmu! Wanene
ya tayar da mu daga barcinmu?” wannan shine abinda mai rahama yay i wa’adi da
shi kuma mazanni sun yi gaskiya”
Wato
mutuwa tamkar barci ta ke kamar yadda wannan aya ke bamu labarin cewa a ranar
lahira kafirai idan an tashe su a rayuwa ta biyu bayan wannan, sais u yi
korafin wa ya tashe su daga barcinsu, wato mutuwarsu. Wani gagarumin abu da
Allah ya ta'allaka da barci kuma shine Mafarki, shi mafarki ba a banza aka hore
mana shi ba sai don Allah ya dada tabbatar mana da cewa duk abubuwa da annabawa
su ka zo dashi don kira da gargadi da sakamakonsu gaskiya ne (wato yadda
rayuwar lahira za ta kasance). A cikin mafarke-mafarken mu, duk da cewa muna
kwance a wani gefe guda sai rayukanmu su rika yin abubuwa na ban mamaki da a
zahiri ko kusa ba za mu iya yi ba. Haka nan muna iya jin dadin gaske a mafarki
(cin abinci ko jima'i ko farin ciki) ko kuma mu fuskanci matsananciyar wahala
(yunwa, asara ko fargaba) yadda muna farkawa za mu ci gaba da jin abinda
ya faru a mafarkin kafin mu gane cewa ashe mafarki ne. A takaice dai Allah
na son mu fahimci cewa barci, mafarki da farkawa a kullum rana da Allah ya
wajbata a tsarin rayuwarmu, an yi su ne domin su rika tuna mana ko jaddada mana
rayuwar duniya, mutuwa da rayuwar lahira ne.
Comments
Post a Comment