RUMFAR SAMA’U
Allah ya samar da ruwa wanda ya rarraba shi wuri-wuri,
kuma kasancewar ruwa yana cudanya da kusan komai kuma yana wanzuwa cikin yanayi
guda uku wato a matsayin turiri ko ruwa-ruwa ko kuma dunkule. Wannan ya haifar
da kusan duk ruwan da Allah ya halitta a duniya na nan sai dai kawai kasancewar
yana zagaye a tsakanin halittu masu rai da marasa rai (wato water circle).
Bayan samar da ruwa sai kuma Allah ya halicci wata rumfa wadda ita ce zata
tsare dukkan halittu da zasu zauna a doron kasa. Allah ya bamu labari cikin
suratul Anbiya inda yake cewa
“Kuma mun sanya sama rufi tsararre”
Wato a farkon duniya bayan an halicci ruwa, da Allah ya
yi halitta kai tsaye to, za ta sami illa yadda ba za ta iya rayuwa ba
saboda tsananin zafi da kuma zaruruwan ultravoilet da ke isowa doron
duniya kai tsaye. Wadanda idan babu wata kariya cikin dan lokaci kankani za su
iya kone halilttu a doron kasa. Don haka sai Allah ya halicci wata rumfa don
kare halittun da zasu zo. Ita wannan rumfa (Ozono layer) ba ma iya ganinta saboda
da iska Allah ya gina ta. Kuma Allah ya samar da ita ne sanadiyar zafin rana
da ke dukan kwayoyin iskar da muke shaka a yanzu wato Oxygen. Idan
wannan iska ta dahu sai ta canza zuwa wa ta irin iska da ake kira Ozone.
Ita Ozone tayi cincirindo ne a tsakanin mil goma zuwa mil talatin a sararin
sama, aikinta shine ta rika tace zaruruwan ultravoilet da ke da illa ga
halittu, ta na mayar da su can sama wato ta haskaka su baya (Reflecting). Idan rana
ta zuro haskenta wanda a ciki kashi 50% ne kawai haske, ragowar zafi
ne da kuma zaruruwan ultravoilet, yayin da suka iso sararin samaniyar duniya
sai kashi 15% daga ciki wannan rumfa ta haskaka shi baya ta hana shi isowa
doron duniya. Kashi 85% ragowar da ya samu isowa doron duniya kuma sai halittu
su zuka domin tafiyar da rayuwar su. Su kuma ragowar kashi 50% na zafi da
zaruruwan ultravoilet suma sai kashi 25% ya zama wannan rumfa ta haskaka su
baya inda suka fito ragowar kashi 75% kuma sai kwayoyin iska (Gases) da ke
sararin duniya su zuke su, wanda sakamakon haka sai kwayoyin iskar su dahu su
rika fitar da tururin infrared wanda wani daga ciki sai ya koma can sararin
sama wani kason kuma sai ya doso doron kasa don dumamata. Ta wannan tsari
sai ya kasance halittu a doron kasa sun sami kariya daga tsananin zafi wanda ya
sa yanayin dumin duniya (Global temperature) ya kasance akalla mizanin zafi
(Degree) 15 a ma'aunin zafi na centigrade. Wannan shi ne yasa halittu ke
zaune a cikin yanayi na ni'ima kuma a ka sami yanayin damina, bazara da
hunturu. Sabanin sauran duniyoyi makwabtanmu kamar su mercury wadda bata da
irin wannan rumfa don haka babu wata hanya ta daidaiton yanayi a kanta don haka
shi yasa da rana a wannan duniya ta mercury yanayin zafi yana kai 800 a
ma'aunin zafi na centigrade, wato ya ninninka wajen da aka taba samun zafin da
ya fi na ko'ina a duniya cikin hamadar Libya da ya nuna zafin da ya
kai degree 102. Sannan da rana ta fadi a wannan duniya sai ta huce ta ma fara
daskarewa domin kafin gari ya waye ma'aunin ya kan kai kimanin degree 300 kasa
da sifili (below zero) wato ya ninninka sanyin cikin kankara sau
daruruwa. Irin wannan zafi da sanyi dake waccan duniya ta Mercury ya
hana wanzuwar ruwa a matsayin ruwa-ruwa (liquid) sai dai a matsayin turiri ko
kankara, Inda ko babu ruwa ai maganar halitta irin tamu bai ma taso ba. A cikin
'yan shekarun nan masana ilimin yanayi sun gano cewa Dan Adam da kansa yana
kokarin rusa wannan rumfa da Allah yayi don kare mu, domin sun gano
cewa sakamakon abubuwa da ake yi a doron kasa irin su kone-konen dazuzzuka
da dattin masana'antu sun haifar da huhhujewa ta wannan rumfa. Duk da
cewa akwai abubuwa daga Allah dake taimakawa a wannan matsala kamar su aman
wutar dutse da numfarfashin halittu, bai sa wannan rumfa cikin hadarin da take
ciki ba tsawon miliyoyin shekaru da take amma cikin shekaru dari biyu kawai da
Dan Adam ya fara aiki da masana'antu ya jawo hujewar kusan kashi uku na wannan
rumfa. Wasu na iya cewa kai ai babu yawa ma abinda ya huje. To ga abinda
sakamakon haka ya haifar: An sami dumamar yanayi yadda zafin duniya ya ke ta
karuwa (Global warming) wanda ya haddasa canzawar yanayin damina
da na rani da na hunturu domin kasashe irin su Nijar na samun ambaliyar
ruwa wasu na kurmi daminarsu na ta raguwa, kasashen sanyi na fuskantar
barazanar matsanancin zafi (cikin yan shekarun nan anyi zafi a Ingila da mutane
da dama suka yi ta mutuwa). Me kake tsammani idan aka wayi gari dusar kankara
na sauka a arewacin Nijeriya? Haka nan samun karuwar zaruruwan ultravoilet da
ke isowa doron duniya yana haifar da ciwon kansar fata. Wutar daji ta zama wata
babbar annoba dake damun kasashe. Duk wannan fa kawai kaso uku ne ya jawo.
Masana sunyi hasashen cewa idan ba a rage kone-kone da dattin masana'antu ba
nan da shekara ta 2050 kashi shida na wannan rumfa zai tafi kuma zai saka gejin
tekunan duniya ya karu da 'yan mitoci wanda hakan zai saka garuruwa dake bakin
teku irinsu Lagos su koma karkashin ruwa, filayen noma su gushe domin
tuddan kankara da ke doron duniya na kudu (Antarctica) da na arewa (Arctic) da
kuma manya tsibiran kankara (Glaciers) zasu narke su tumbatsa tekunan duniya.
Masana na ta kiraye-kirayen a yi hattara amma Amurka, wadda ita tafi kowa
gurbata sararin samaniyarmu ta yi kunnen uwar shegu da daftarin Kyoto (Kyoto
protocol) wanda ke kira ga kasashe masu arzikin masana'antu su yi gaggawar rage
dattin masana'antunsu. Domin yin hakan inji masana zai iya saka wannan rumfa ta
koma ta dinke kanta. Samar da wannan rumfa, wadda take daya daga cikin
manyan ginshikan da ke tsare rayuwar halittu a doron kasa, yanzu da hannun
mu muke neman ruguza ta. Muddin ba muyi gyara cikin gaggawa ba to koda mun
tsallake bala'in da wannan zai haifar tabbas ne Ya'yanmu su biya daga
tabargazarmu.
Comments
Post a Comment