SHIN AKWAI ALLAH?
Mafi
shahara cikin masana kimiyya a tarihin duniya, Albert Einstein, ya yi wasu
maganganu guda biyu: Na farko “Kimiyyar
da babu addini gurguwa ce sannan addini ba tare da kimiyya ba makaho ne” sannan
ya ce “Kimiyya na iya bayanin yadda
abubuwa su ke a zahiri amma ba za ta iya bayanin dalilin kasancewa yadda su ke
ba” Addini da kimiyya sun kasance abubuwa guda biyu da su ka fi komai
tasiri a rayuwar Dan Adam, duk da cewa kowanne akwai irin mahangarsa. Don haka
ya kamata mu fahimci cewa abubuwa ne masu cikakkiyar alaka tamkar dai fuskoki
guda biyu na kwabo. Alal misali mun san a kimiyance yadda sammai da kasa su ka
samu kimanin shekaru biliyan 13 da su ka wuce daga tarwatsewar Big Bang, amma
kimiyya ba ta da bayanin dalilin samuwar wannan sammai da kassai, addinai kadai
ke iya wannan bayani. Mun san cewa a kimiyance duk hasken da ya daki madubi,
kashi 95% ya kan dawo baya (reflect) amma kimiyya ba ta iya gane dalilin da ya
sa ragowar kashi 5% ke ratsawa ta cikin madubin ya wuce. Don haka kimiyya na
iya mana bayanan dalilan da abubuwa ke wanzuwa yadda su ke amma addinai ke iya
bayanin me yasa hakan ke faruwa.
Idan mu ka dauki Dan Adam, mun san ya na kasancewa cikin tagwayen tsarin jiki da ruhi. Jiki na kasancewa tsani na wanzuwar rayuwarsa, amma rai ke sako shi cikin tsarin (wato lokacin haihuwarsa) ko kuma ya cire shi cikin tsarin (lokacin mutuwa). Kimiyya na iya nazarin jikin Dan Adam ta kowanne fanni amma ba ta iya nazarin ruhi, domin ya zarce gwadaben da ta ke da iko. Wannan dalili ya tabbatar da cewa duniya na karkashin tsarin zahiri da badini. Amma kasancewar masana kimiyya sun sami damar iya nazarin duk abubuwa na zahiri su fahimci tsarinsu, sai wasu ke ganin ai babu dalilin cewa badini na da wani tasiri don haka ma su ke ganin cewa babu Allah.
Shin Akwai Allah? Tabbas akwai Allah. To amma shin muna da bukatar sai an tabbatar da hujjar cewa ya na nan a zahirance? A’a, domin kamar yadda ba ma iya tabbatar da samuwar ruhi (ko rai) a zahirance haka nan babu yadda za’a iya tabbatar da samuwar Allah a zahirance domin shi ba jiki ba ne don haka duk wata hanyar sadarwa ta zahiri da muke da ita ba za ta iya tsinkayar Allah ba. Amma a hankalce da hujjoji masu karfi na zahiri karkashin ilimin kimiyya Allah da kansa ya tabbatar mana da samuwarsa ta hanyoyi guda hudu:
1. Shi kadai ke iya samar da rai-
Q21:30
“Shin kuma wadanda su ka kafirta, ba su gani cewa lallai...kuma mun halicci
dukkan mai rai daga ruwa?”
Allah
a cikin wannan aya ya tabbatar mana da cewa shine ya halicci duk wani abu mai
rai, don haka duk wani wanda ke ja da wannan hurumin na Ubangiji sai Allah ya
kalubalance shi a Qur’ani da cewa
Q22:73
“Ya ku mutane! Ga wani misali ku saurara zuwa gare shi, lalle ne wadanda ku ke
kira baicin Allah, ba za su iya halitta kuda ba, ko da sun taru gare shi”.
Hakika
kimiyya ta fahimci yadda rayuwa ta samu a doron wannan duniya tun daga farkon
lokaci a ruwa, amma kuma kimiyyar ta gaza wajen gane daga ina wannan rayuwa ta
samo asalinta. Matsalar gano daga inda rayuwa ta samo asali a wannan duniya a
kimiyance, ya zama kasawa domin cikin masana kimiyya da ke kan gaba wajen
wannan bincike, wato Stanley Miller cewa ya yi “Hakika asalin rayuwa a wanna
duniya ya zama abu mafi shiga duhu a gare ni da sauran mutane”. Shi kuma Simon
Conway cewa ya yi “An kasa kirkirar sabon rai a dakunan binciken kimiyya, kuma
babu wata alama za’a iya yin hakan a nan gaba…samuwar rai a wannan duniya ya
zama mu’ujiza”. Shi ma wani shahararren a wannan fannin na binciken asalin rai,
Francis Crick cewa ya yi “Duk wani mai gaskiya, wanda ke da masaniyar ilimin da
muke da shi a yanzu, zai yadda cewa samuwar rai kawai mu’ujiza ce”. Shi ma
masanin Falsafa Karl Popper cewa ya yi “Ci gaban da aka samu game da ilimin
halittu masu rai, maimakon ya haskaka yadda rayuwa ta fara samuwa sai ma ya
dada tura abubuwa cikin duhu”.
Cikin
Babban kundin nazarin halittu masu rai (Encyclopedia of the Biological
Sciences) masanan kimiyya wadanda su ka nakalci kowanne fanni da ya jibinci
ilimin halittu masu rai da kansu cewa su ka yi “Tsarin yadda halitta ta samu a doron duniya daga abubuwa mara sa rai
sau daya ya taba faruwa, kuma duk wani yunkuri na kokarin samar da kowacce irin
halitta mai rai a dakunan binciken kimiyya ya gagari masana”
Tsarin
kimiyyar Asalin Halitta na Charles Darwin, duk da gagarumar fahimta da ya kawo
cikin nazarin asalin halittu, bai iya kawo wani bayani game da daga ina rayuwa
ta samu ba. Duk aikin Darwin ya kebanta ne daga yadda halittu su ka habaka,
wato ya fara aikinsa ne bayan samuwar rayuwa. Shi kansa Darwin bai yi kokarin
kutsawa cikin wannan lamari na asalin rai ba, Babban abinda ya sa ka tsarinsa
karo da masu addini shine na kawar da hannun Allah cikin samuwar rai. Micheal
Ruse ya yi tambaya cewa “Menene ruhi ne? Dutse ba shi da rai, matacciyar saniya
ta rasa na ta ran, ni da kai mu na da shi (rai)”
Q17:85
"Su na tambayar ka game da ruhi, ka ce “Ruhi daga al’amarin Ubangiji na
ne, kuma ba a baku (kome) ba daga ilimi face kadan"
Wannan
tambaya ta Micheal Ruse ta dade a zuciyar mutane kuma a lokacin Annabi Muhammad
(SAW) da mutane su ka damu da irin wannan tambaya sai Allah ya saukar da wannan
aya da ke tabbatar da cewa duk ilimin da Dan Adam zai samu a game da rai ko
ruhi, sai dai ya fahimci kadan daga cikin sirrin domin hurumi ne na Allah ba
wanda ya isa ya san wani abu face dan kalilan da Allah ya sanar.
Tarihi
ya tabbatar mana da gazawar mutum dangane da bincike kan ruhi, wato an kasa
samun wanda zai iya kirkirar rai ko kuma ya fadi yadda ya ke ko daga ina ya ke.
Cikin dan ilimin da Allah ya sanar da mu game da ruhi shine fadarsa cikin
Qur’ani.
Q15:28-29
"Kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce wa Mala’iku “Lalle ni mai hallittar
wani jiki ne daga kekasashshen yumbu wanda ya canza. To idan na daidaita shi
kuma na hura daga Ruhina a cikinsa, to ku fadi a gareshi kuna masu yin sujada”
Cikin
wannan aya sai Allah ya bamu labarin yadda ya fara halitta sannan kuma ya fadi
yadda rai ya ke da inda ya samo asali. Wato kamar yadda masana kimiyya
bincikensu ya nuna musu cewa rayuwa ta faro daga abubuwa mara sa rai, abinda
Allah ya tabbatar mana a nan cewa daga yumbu ne wanda ya bi wasu matakai na
canji, ya tsara yadda rayuwa ta fara amma bayan surantawa sai da ya busa
ruhinsa ga wannan sura sannan ta fara rayuwa. Wato ruhi ko rai ya samo asali
daga ruhin ubangiji, kasancewar Allah ba jiki ba ne don haka sai ruhinsa wanda
ya samar da rayukan mu ya kasance da dab’iu irin na kudirar ubangiji yadda bama
iya jinsa ko ganinsa balle mu taba shi. Abinda kawai mu ka sani shine cewa mu
na iya gane idan akwai shi (rayuwa) ko idan babu shi (mutuwa).
Tun
kafin zuwan musulunci, Allah ya bada irin wannan labara cikin Attaura a cikin
littafin Farawa inda ya ce
Genesis 2:7 “Ubangiji
ya halicci mutum daga kasa sannan ya hura a cikin hancinsa ruhi: Sai ga mutum
ya rayu”
Sirrin
rayuwa shi ne ta samo asali daga ruhin Ubangiji, kuma ba Adam kawai ya sami
wannan busar ruhi ba, duk wata halitta da Allah zai halitta sai ya busa mata
wannan ruhi kafin ta fara rayuwa domin shi kadai ke da wannan hurumi.
Allah
ya kara tabbatar mana da hakan cikin
Q32:9 “Sannan ya
daidaita shi, kuma ya hura a cikinsa daga ruhinsa kuma ya sanya muku ji da gani
da zukata”
Wancan
kalubale na Ubangiji cewar idan wani na tantamar cewa babu Allah ko kuma ba shi
ya halicci komai ba, na nan har gobe. Zuwa yanzu dai mun gamsu da cewa masana
kimiyya da su ka fi kowa shahara da wadanda su ka sadaukar da lokacinsu wajen
neman yadda za’a iya samun rai daga dakunan bincike, da bakinsu sun karbi
gazawarsu. Don haka duk wanda ke son mu yarda cewa babu Allah, abinda zai yi
kawai shine ya karbi kalubalen Allah ya samar mana da rai kamar Kuda, idan ya iya
yin haka sai mu sallama masa.
Comments
Post a Comment