TSUNTSAYE

Allah ya ce mana

Q67:19" Shin basa ganin tsuntsaye dake samansu yadda  suke (tashi) da kada fukafukansu? Babu mai iya rike su face Allah mai rahama"

Tsuntsaye na daga cikin halittun dabbobi da suka fi burge Dan Adam, saboda su kadai ne dabbobi masu gashi da fukafukai da ke iya tashi sama. Ko da yake dai ba dukkan tsuntsaye ne ke tashi ba (kamar Jimina d.s.s). Tsuntsaye na saka kwai ne wajen haihuwa, kuma da yake Allah ya halicci jikinsu da yanayin dumi irin jikin mutane (Warm blooded) wannan ya basu damar iya rayuwa a mabanbantan muhallai (kamar kankara, hamada, kurmi d.s.s.). Suna iya tashi sama sosai yadda har su zarce manyan tsaunuka ko kuma yin nutso cikin ruwa na tsawon mita 250. Dukkan jikinsu a lullube yake da gashi kuma gashin yana fitowa ne a kan wani dogon holoko mai kama da kumba (wanda ake kira keratin). Shi wannan abu da shi ne Allah ke halittar farata da gashi a jikin mutum. Wannan holokon abu yana da karfi sosai amma kuma bashi da nauyi (tamkar dai farce) don haka ya taimaka wajen tashi sama.

Fukafukan tsuntsaye an rike su da wasu karfafan kwanji dake kirjinsu tare da taimakon wasu irin gurin-guntsi da ke hada su da fukafukai. Kirjin tsuntsaye Allah ya suranta shi tamkar yadda karkashin kwale-kwale yake wanda hakan ya taimaka wajen iyo a sararin sama. Suna iya tashi sama ne ta hanyar kada fukafukansu, wato yayin da suka kada fiffikensu kasa sai ya kasance sun danna iska kasa kenan, ita kuma iska sai ta daga fiffiken sama. Yayin daga fiffiken sai su gasusuwan-tashi su karkace kowanne ya kwanta kan na kusa dashi ta yadda iska ba za ta iya ratsa tsakaninsu ba, ta haka fukafukan nasu baza su yi musu nauyin dagawa ba. Amma yayin daga fuffuken sama kuma sai su wadannan gasusuwan tashin su baje yadda iska zata iya ratsa su domin kada dai fiffiken yayi nauyi (misali idan ka dauki mafici guda biyu da mai huji da mara huji idan kana son ya daga sama zaka ga cewa mai hujin yafi sauki saboda rashin nauyi). Tsuntsaye na da fukafukai iri-iri wanda ke banbanta yadda suke tafiyarsu a sama. 'Yan gajeru kuma kewayayyun fukafukai na baiwa masu su sauri da gaggawar motsawa amma fadada kuma dogwaye suna amfani ga masu tashi can sama kuma suke kwanciya kan iska (gliding).

Jela ita ma na da mahimmanci wajen kula da nahiya ko bangaren da tsuntsu ke son juyawa da kuma wajen yin burki yayin sauka ko rage gudu. Tsuntsaye kan karkata jelarsu su kuma daga fiffike daya yafi daya yin sama wajen yin kwana. Wajen burki ko sauka kuwa sai su lankwasa jela ta kalli wajen cikinsu. Gaba dayan halittar tsuntsu idan ka lura zaka gane cewa komai nasu don su sami saukin tashi akai masu shi. Hatta akasarin kashin da ke jikinsu zaka samu holoko ne kuma basu da hakora duk don dai rage musu nauyi. Sun fi kowacce dabba saurin numfashi (misali tattabara mai kai sako na numfashi 450 a minti guda idan ka gwada da na mutum yayin da yake gudu 160 ne kawai a minti daya). Haka kuma wajen bugawar zuciya,  tasu kan buga daga 400-1000 a minti guda kwatankwacin ta mutum na bugawa sau 70 a minti daya. Idanuwansu kuma suna da wata kariya rubi uku, wato akwai wata fata tamkar yadda ta mutane ke rufe ido gaba daya sannan daga ciki sai wata fatar mai kamar tantani da ke rufewa yayin da suke barci. Ta karshe kuma tana kadawa daga wannan gefe zuwa wancan don share da wanke dattin ido da kuma kariya daga iska da hasken rana.

Yawancin dabbobi nayin kaura amma babu masu hijira kamar ta tsuntsaye. Suna da agogo da aka halicce su dashi dake sa su gane lokaci, sannan suna da basirar yin amfani da motsin rana wajen gane nahiyar da suke. Misali idan suna arewacin duniya (Northern hemisphere) suna gane cewa sha biyun rana ta yi don zasu gane cewa rana ta karkata wajen kudu-kudu. Da daddare kuma suna yin amfani da tsarin yadda taurari suke a sama don su tantance kudu ta hakika (True North). Yayin hijira kuma suna amfani da wani sinadari da ke cikin kwakwalwarsu (magnetite) da ke basu damar amfani da sararin maganadisu (Earth magnetic field) don gane nahiya. Akwai wani tsuntsu (Golden Plover) da kan iya yin tafiyar kilomita 3200 yana keta teku ba tare da ya sauka ba. Masu doguwar tafiya irin wannan kan gane lokacin da iska ke dogon zango don haka idan sun tashi sama yawancin tafiyar kwanciya kawai suke kan iska ba tare da kada fukafukansu ba. Wani abin al'ajabi shine wasu tsuntsayen kan kekashe kwansu a mashekari kuma su tafi su bar 'yayan, amma da 'yayan sun isa tashi sai su bi iyayen zuwa inda suke ba tare da wani dan jagora ba. Akwai ma wasu tsuntsaye da aka saka cikin irin jirgin yakin nan na Birtaniya da ya tashi zuwa gabas mai nisa aka dinga sakin su daga gari-gari, amma cikin su sha biyu sai da goma suka koma Birtaniya kuma akwai wanda yayi tafiyar sama da kilomita 3000. Akwai wasu jemagu a nan Kano da ke zuwa England duk shekara su dawo kuma an gane haka bayan daura shaida a kafafun wasu daga ciki a can England amma aka gansu kuma a Kano tare da wannan shaida. Fahimtar yanayin tsuntsaye dole ne ya sa mutum ya dada tabbatar da waccan aya da ke cewa banda Allah babu mai iya rike su don haka ayi nazari

 

Comments

Popular posts from this blog

HUJJOJIN TASHIN KIYAMA A KIMIYANCE

WUTA

RUWAN DUFANA