SHIN AKWAI ALLAH?

Mafi shahara cikin masana kimiyya a tarihin duniya, Albert Einstein, ya yi wasu maganganu guda biyu: Na farko “Kimiyyar da babu addini gurguwa ce sannan addini ba tare da kimiyya ba makaho ne” sannan ya ce “Kimiyya na iya bayanin yadda abubuwa su ke a zahiri amma ba za ta iya bayanin dalilin kasancewa yadda su ke ba” Addini da kimiyya sun kasance abubuwa guda biyu da su ka fi komai tasiri a rayuwar Dan Adam, duk da cewa kowanne akwai irin mahangarsa. Don haka ya kamata mu fahimci cewa abubuwa ne masu cikakkiyar alaka tamkar dai fuskoki guda biyu na kwabo. Alal misali mun san a kimiyance yadda sammai da kasa su ka samu kimanin shekaru biliyan 13 da su ka wuce daga tarwatsewar Big Bang, amma kimiyya ba ta da bayanin dalilin samuwar wannan sammai da kassai, addinai kadai ke iya wannan bayani. Mun san cewa a kimiyance duk hasken da ya daki madubi, kashi 95% ya kan dawo baya (reflect) amma kimiyya ba ta iya gane dalilin da ya sa ragowar kashi 5% ke ratsawa ta cikin madubin ya wuce. Don haka...