Posts

RUKUNIN TAURARONMU-RANA

Image
  Rana tauraro ce tamkar sauran taurari amma kasancewar ita ce tauraro mafi kusa da mu, shi ya sa muke ganinta da girma fiye da sauran taurari sannan kuma muke jin zafin ta. A tsari irin na taurari, Rana tauraro ce ta tsaka-tsaki, wato akwai wadanda suka ninninka ta akwai kuma wadanda basu kaita ba a bangaren zafi da haske. Allah ya ce mana cikin suratul Anbiya Q21:33 “Shine wanda ya halicci rana da wata. Dukkansu suna yin iyo ne cikin wani sarari” Wato a wannan tsari rana da wata dukkansu na motsawa sannan ita ma duniyar mu tana motsawa. Rana tana kewayen tsakiyar wannan dabaka da muke ciki (Milky way galaxy) sau daya duk bayan shekaru miliyan 250, kuma ta kasance a cikin gungun taurari (cluster) wadanda basu kusanci tsakiyar wannan dabaka tamu ba, kuma basu yi waje da nisa sosai ba (dabakar mu tana da fadin da tafiyar da haske zai yi ne a shekaru miliyan 100). Hakan shine ya bawa halittu damar iya rayuwa a doron duniya, domin da rana ta kusanci tsakiyar dabaka, saboda cunko...

HUJJOJIN TASHIN KIYAMA A KIMIYANCE

Image
Hausawa na cewa “komai ya ke da farko yana da karshe” haka nan cikin suratul Nasr Allah ya tunatar da mu cewa Q103:1-2 “Ina rantsuwa da lokaci (time) lalle ne mutum yana cikin hasara” Wadannan maganganu na sama, idan muka yi musu duba na nazari zamu gane cewa hakika duk wata halitta a doron kasa tana gaggawa ne izuwa karshenta. Yadda a farkon lokaci babu kowa haka ma za’a wayi gari komai ya kare wata rana. Cikin ginshikan imani, Allah ya wajabta yarda da ranar lahira kuma babu wani addini da bai jaddada haka ba, amma akasarin mutane na jayayya da cewa idan an mutu za’a tashi. Allah cikin hikimarsa ya bamu hujjoji na kimiyya a warwatse cikin Qur’ani wadanda suke tabbatar mana da cewa lallai kiyama gaskiya ce. Bari mu duba wadannan hujjoji daki-daki. A farko dai Allah ya fara da jan hankalin mu cikin suratul A’araf Q7:185 “Shin ba su yi duba ba a cikin tsarin sammai da kasa, da kuma dukkan abin da Allah ya halitta, kuma akwai alamun kasancewar ajalinsu, hakika, ya matso? To da wa...

LANTAR-MAGANADISU

Image
  Wani muhimmin al'amari da yake shima babban ginshiki ne wanda Allah ya samar domin tafiyar da rayuwa ta abubuwa masu rai da marasa rai, shine lantarki da maganadisu. A cikin surayul yasin Allah yana cewa Q36:36" Tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya halicci nau'i bibbiyu na abinda ke fita daga kasa, da su kansu (mutane) da ma abinda ba su sani ba" Ya halicci dukkannin halittu a tsari mai biyu-biyu, wato babu wata halitta da bata da kishiya. Ba ma halitta da muka sani ba Allah na cewa a cikin abubuwa da ya halitta wadanda ma bamu sani ba duk wannan tsari na bibbiyu suke bi. Hikimar wannan shine domin Allah ya tabbatar wa kowa cewa shi kadai ne tilo da bashi da abokin tarayya. Lantarki da maganadisu suna cikin hikimar Allah na tsara abubuwa bibbiyu, kuma suna daga cikin farkon abubuwan da Allah yafara halitta, domin dai bayan samar da kwayar zarra wadda ita ce bulon ginin kowacce halitta mai rai da mara rai, lantarki da maganadisu sune ginshikan da ke dauke da kwa...

JUJJUYAWAR ISKOKI

Image
Iska kamar ruwa da wuta ginshiki ce ta rayuwar dukkan halittu walau dabba ko tsirrai. Masana sun rybuta dubban littattafai akan yanayin iskoki, kuma a kullum suna kara fahimtar ta da irin amfanoninta. Allah kansa yayi mana bayanai iri-iri cikin Qur’ani a game da iska. Misali cikin suratul Jasiya Q45:5 “Da jujjuyawar iskoki, akwai ayoyi ga mutane masu hankali” Juyawar iskoki a doron duniya al’amari ne da dole ya burge duk wani mahaluki da ke amfani da kwakwalwarsa don yin tunani, domin akwai tsari da ka’idoji da suke bi. Juyawrsu ta ta’allaka ne akan yanayin zafi ko dumi (temperature) na sashe ko nahiyoyi. Shi yanayin zafi/dumi na samuwa ne kai tsaye daga zafin rana. A yayin da zaruruwan zafi (heatwaves) da ke sauka daga rana, su kan dafa wani sashe na iska. Nan da nan sai ita dafaffiyar iska ta doshi inda yake da sanyi, wato idan ta sama ce sai ta doshi kasa idan kuma ta kasa ce sai ta doshi sama, haka nan idan ta gaba ce sai ta doshi baya idan kuma ta baya ce sai ta doshi gaba. A loka...

KUDAN ZUMA

Image
  Kwari su ne jinsin dabbobi da suka fi kowacce dabba yawa a wannan duniya tamu. Ana samun su a kusan kowacce nahiya, kuma ayyukansu don amfanin rayuwar Dan Adam ba zai misaltu ba. Su ma ba’a bar su a baya ba cikin irin halittun da Allah yayi mana bayanin su cikin Qur’ani. Allah ya kawo mana maganganu a kan kuda, kudan zuma, tururuwa, gizo-gizo da sauransu. Dukkan abinda Allah ya ambata cikin Qur’ani zaka idan kayi bincike tarar daa shi da cikakken tsari na kimiyya wanda kafin zuwan Qur’ani babu wani cikakken bayani na kimiyya a kansa. Bari mu duba kudan zuma, saboda babu wani kwaro da masana kimiyya suka yi bincike a kansa kamar shi. Cikin suratul Nahli Allah yace Q16:68 “Kuma ubangijinka yayi wahayi zuwa ga kudan zuma cewa “ka riki gidaje daga duwatsu, kuma daga itace, kuma daga abinda suke ginawa ” Wannan aya ta fara da tabbatar mana da cewa dabbobi ma ana yi musu wahayi, domin ba don wannan wahayi ba ta ina zasu rika tafiyar da rayuwarsu a tsare kuma cike da ilimi? Shi wa...

SAMAR DA JARIRI

Image
Idan mun fahimci yadda ake samar da jariri abu na gaba da ya kamata Dan Adam ya fahimta shine yaya gangar jikinsa take. Allah ya ce mana cikin suratul Tin  95:4 “lalle mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa”  A halittun duniya babu wanda ya kai Dan Adam kyawon siffa sannan jikinsa yafi kowanne irin mashin da ka sani. Akwai yan rahoto (Receptors) miliyan hudu warwatse jikin fatarmu da ke banbance mana zafi, sanyi, tabawa ko ciwo. Fatarmu an yi ta rubi biyu don kare jiki daga bushewa da kuma adana ruwa da ke cikin jiki. Tana mana kariya daga sinadarai masu guba da kuma yanayi na sanyi ko zafi ta hanyar daidaita dumin jikinmu (temperature). A cikin bakin mu kan harshe, akwai kananan hudoji guda dubu tara wadanda ke taimaka mana banbance dandanon zaki, gishiri, tsami da sauransu. Jikin mutum na dauke da silin gashi miliyan biyar, wanda kowanne na iya Rayuwa ta akalla shekara 7. Wannan gashi, idan banda ta hanyar konewa, yana da wahala a iya lalata shi ta hanyar danshi ko ru...